Mojtaba Khamenei Ya Gargadi Trump a Sakon Sallah, Iran Ta Harbo Jirgin Amurka

Mojtaba Khamenei Ya Gargadi Trump a Sakon Sallah, Iran Ta Harbo Jirgin Amurka

  • Yayin da sabon rikici ke son barkewa, Mojtaba Khamenei ya ce kasashen Gabas ta Tsakiya ba za su sake zama mafaka ga sansanonin sojin Amurka ba
  • Tun bayan hawansa matsayin jagoran addini mafi girma na Iran, Mojtaba bai taba fitowa a bidiyo ko a gaban kyamara ba amma ya sha tura sakon gargadi
  • A daya bangaren kuma, rundunar IRGC ta Iran ta ce ta harbo jirgin MQ-9 Reaper na Amurka, ta kuma harbi F-35 da jirgin leken asiri a sararin samaniyarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi gargadi a ranar Talata cewa kasashen yankin ba za su sake zama garkuwa ga sansanonin sojin Amurka ba.

A gargadin da ya yi, Mojtaba Khamenei ya ce Amurka ba za ta sake samun wata mafaka mai aminci a Gabas ta Tsakiya ba.

Kara karanta wannan

Fasto ya taro rigima da Sheikh Jingir kan APC ta ba Musulmi takara a Jos

Mojtana Khamenei na kasar Iran
Jagoran addini na Iran a hagu, wani jirgin yaki a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadin Mojtaba Khamenei ga Amurka

Al Jazeera ta ce Mojtaba ya yi magana ne bayan da sojojin Amurka suka tabbatar da kai hare-haren da suka kira “kare kai” a Kudancin Iran duk da tattaunawar da ke ci gaba.

“Abin da ya tabbata a wannan batu shi ne hannun agogo ba zai koma baya ba, kuma al’ummomi da kasashen yankin ba za su sake zama garkuwa ga sansanonin Amurka ba,”

- In ji Khamenei a sakon babbar Sallah.

An lura cewa har yanzu bai fito a fili a bainar jama’a ba tun bayan da ya karbi mulki bayan kisan mahaifinsa a watan Maris, 2026.

Ya kara da cewa Amurka na rasa tasiri a yankin, yana mai cewa:

"Tana kara nisa da matsayinta na da a kowace rana da ta wuce.”
Shugaba Donald Trump
Donald Trump na yi wa Amurkawa jawabi a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta harbo jirgin Amurka

Rundunar IRGC ta ce tana da cikakken hakki na ramuwar gayya kan duk wani keta tsagaita wuta da Amurka ta yi, kamar yadda kafafen gwamnati suka ruwaito.

Kara karanta wannan

Bikin sallah: Gwamna Zulum ya raba shinkafa mai dauke da hoton Tinubu

Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ta ce ta harbo jirgin MQ-9 Reaper bayan gano wani jirgin sama mai tayar da hankali da ya shiga sararin samaniyar Iran a yankin Tekun Fasha a ranar Talata.

Jerussalem Post ta ce Iran ta ce ta harbi jirgin yaki na F-35, wanda ya tilasta masa ficewa daga sararin samaniyarta, haka kuma ta kai hari kan jirgin leken asiri na RQ4.

IRGC ta kara da cewa ba za ta yi wasa ko sakaci wajen mayar da martani kan keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta yi ba.

Sojojin Amurka sun kai hari Iran

A wani labarin, mun kawo muku cewa Amurka ta kai hari Kudancin Iran cikin dare, inda ta ce ta kai farmaki kan jiragen ruwa da ke kokarin dasa nakiyoyi.

Kyaftin Tim Hawkins na rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ya ce sun kai hare-haren ne domin kare kai daga barazanar Iran a Kudancin kasar.

Ya kara da cewa rundunar kasar Amurka na ci gaba da kare dakarunta a Iran duk kokarin da ake domin ganin an cimma yarjejeniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng