Ana Maganar Arafa, Donald Trump Ya kai Hari Kasar Iran
- Sojojin Amurka sun ce sun kai sababbin hare-hare a Kudancin Iran, inda suka kai farmaki kan wuraren makamai masu linzami
- Rundunar Sojin Amurka ta bayyana a wata sanarwa cewa an kai hare-haren ne domin “kare kai”, kuma an tsara su ne domin kare sojoji
- Kakakin rundunar, Kyaftin Tim Hawkins, ya ce sojojin Amurka na ci gaba da kare dakarunsu tare da yin takatsantsan domin cimma yarjejeniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Rahotanni sun nuna cewa cewa dakarun Amurka sun kai hare-hare kan wasu wurare a Kudancin Iran bisa umarnin shugaba Donald Trump.
Bayanan da aka samu daga Amurka sun nuna cewa sojojin kasar sun kai hare-hare a kudancin Iran a ranar Litinin yayin da ake shiye-shiryen ranar Arafa.

Source: Facebook
Amurka ta kai hari Iran
Al Jazeera ta wallafa cewa, kakakin Rundunar sojin Amurka, Tim Hawkins ya yi magana bayan harin, inda ya ce:
“Dakarun Amurka sun dauki matakin kare kai a yau domin kare sojojinmu daga barazanar da dakarun Iran ke haifarwa.”
Ya kara da cewa:
“Abubuwan da aka kai wa hari sun hada da wuraren harba makamai masu linzami da kuma jiragen ruwan Iran da suke kokarin dasa nakiyoyi.
"Rundunar na ci gaba da kare dakarunta tare da nuna takatsantsan yayin da ake ci gaba da tsagaita wuta.”
Kamar yadda bayanai suka nuna, kafafen yada labarai na Iran sun bayar da rahoton fashe-fashe a tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas da ke Kudancin kasar, yayin da wani rahoto ya ce an shawo kan lamarin.
Har yanzu Iran ba ta mayar da martani kan sababbin hare-haren Amurka ba. Haka kuma ba a san irin tasirin da za su yi kan batun yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran ba.
Maganar Amurka bayan harin
BBC ta wallafa cewa bayan hare-haren, ministan harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce har yanzu akwai yiwuwar cimma yarjejeniya da Iran.
Ya yi magana yana mai nuni da tattaunawar da aka shirya yi a ranar Talata tsakanin babban mai shiga tsakani na Iran, ministan harkokin wajen kasar, da firaministan Qatar.

Source: Getty Images
Trump ya karrama sojojin Amurka
Shugaba Donald Trump ya karrama sojojin da suka mutu a yakin da Amurka da Isra’ila suka yi da Iran a wani biki da aka gudanar a makabartar Arlington.
Shugaban Amurka ya ce:
“A aikin Operation Epic Fury, mun rasa rayuka 13 masu daraja, mutane na musamman kwarai. Wadannan maza da mata jajirtattu sun sadaukar da rayukansu domin tabbatar da cewa kasar da ta fi daukar nauyin ta’addanci a duniya ba za ta taba mallakar makamin nukiliya ba.”
Netanyahu ya yi waya da Trump
A wani labarin, mun kawo muku cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya shaida wa na kusa da shi cewa ya yi waya da Donald Trump.
Bayan wayar, ya ce wa jami'an shi cewa Isra’ila ba ta da cikakken iko ko tasiri kan shawarar Donald Trump dangane da Iran yayin da aka tsagaita wuta.
Daya daga cikin jami’an Isra’ilan da ke da masaniya kan tattaunawar ya ce Netanyahu ya nuna damuwa kan yarjejeniyar fahimtar juna da ake tattaunawa a yanzu.
Asali: Legit.ng


