Iran Ta Harbo Jirgin Yakin Amurka a Sama, Dakarun Trump Sun Yi Martani
- Ana cigaba da zaman doya da manja tsakanin gwamnatin Iran da Amurka karkshin shugaban kasa Donald Trump duk da tsagaita wutar yaki
- A ranar Alhamis, 28 ga watan Mayun 2026, dakarun Iran sun bayyana cewa sun harbo wani jirgin Amurka da ya shiga sararin samaniyarsu
- Jim kadan bayan fitar da labarin, gwamnatin shugaba Donald Trump ta yi martani, inda ta yi karin haske game da abin da kasar Iran ta fada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Kasashen Amurka da Iran na cigaba da kai wa juna farmaki duk da cewa sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a kwanakin baya.
A 'yan kwanakin nan, Amurka na cigaba da kai hare-hare kan kadarorin Iran, musamman a teku, abin da Tehran ta bayyana da karya ka'idar yarjejeniyar da suka yi.

Source: Getty Images
Kasar Iran ta harbo jirgin Amurka
India Today ta wallafa cewa gwamnatin Iran ce an tare wani “jirgin sama mai hatsari” kuma an harbo shi a yankin Jam da ke lardin Bushehr.
Rahoton, wanda ya ambato gwamnan yankin Jam, Masoud Tangestani, ya ce tsarin kariyar sararin samaniyar Iran ya samu nasarar kai hari kan jirgin.
“Lamarin da ya faru da daddare ya hada da harbo wani jirgin sama mai hatsari,”
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iran ya ambato Tangestani yana bayani, tare da karawa da cewa al’amura sun koma daidai a birnin.
Rahotannin sun fito ne a daidai lokacin da ake fuskantar karin tashin hankali a yankin Tekun Fasha da zama cikin fargaba a Gabas ta Tsakiya.
Hakan na zuwa ne duk da alamun cewa Washington da Tehran na matsowa kusa wajen tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da sassauta takunkumi kan zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz.

Source: Facebook
Rahotanni sun ce har yanzu Shugaban Amurka Donald Trump bai amince da shirin ba, yayin da kafafen gwamnatin Iran suka dage cewa ba a kai ga cimma yarjejeniya ta karshe ba.
Sabbin zarge-zargen sun kuma zo ne sa’o’i bayan da aka ruwaito cewa IRGC ta kai hari kan jiragen ruwa guda hudu da ke aiki kusa da Hormuz, ciki har da jiragen da ake zargin suna da alaka da Amurka.
Amurka ta yi watsi da zargin
Amurka ta musanta rahotannin kafafen yada labaran Iran da ke cewa an harbo jirgin samanta a lardin Bushehr na Iran, inda wani jami’in Amurka ya ce babu wani jirgin saman Amurka da aka lalata kusa da yankin.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito, yana ambaton wani jami’in Amurka, cewa ba a harbo wani jirgin saman Amurka kusa da lardin Bushehr na Iran ba duk da ikirarin tashar talabijin ta gwamnatin kasar.
Khamenei ya gargadi Trump
A wani labarin, mun kawo muku cewa jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei ya gargadi shugaba Donald Trump na kasar Amurka.
Mojtaba ya yi magana game da Trump ne a sakon barka da sallah da ya fitar bayan dakarun Amurka sun ce sun farmaki wani jirgin ruwan Iran.
A bayanan da ya yi, jagoran addinin ya bayyana cewa daga yanzu Gabas ta Tsakiya ba za ta cigaba da zama mafaka ga sojojin Amurka ba.
Asali: Legit.ng


