Gobarar Titi: Yadda Tsawaita Rufe Hormuz ke 'Daga Likkafar Man Najeriya a India
- Rikicin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya ya kawo cikas ga jigilar mai ta mashigar Hormuz, lamarin da ke kara darajar kasuwar man Najeriya
- Yayin da rikicin ke 'kara tsananta, Indiya ta ƙara sayen ɗanyen mai daga Najeriya da wasu ƙasashen Afrika domin samun sauki saboda rufe Hormuz
- Masana sun yi gargadin cewa matsalar Hormuz na iya jawo tashin farashin mai a duniya yayin da Amurka da Iran suka ja daga game da wuce wa ta hanyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Najeriya – Rikicin da ke gudana tsakanin Isra’ila, Amurka da Iran ya haifar da tsaiko wajen jigilar ɗanyen mai ta mashigar Hormuz, lamarin da ya sa Najeriya ta samu ƙarin damar fitar da ɗanyen mai zuwa ƙasar Indiya a ‘yan makonnin nan.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Kotu ta kawo karshen shari'ar Jonathan kan takarar shugaban kasa a 2027
Rahotanni sun nuna cewa matatun mai na Indiya sun fara karkata zuwa kasashen Afrika da Latin Amurka domin samun wadataccen ɗanyen mai bayan da jigilar mai daga Gabas ta Tsakiya ta samu tangarɗa.

Source: Getty Images
Business Insider Africa ta wallafa cewa bayanan kamfanin sa ido kan harkokin kayayyaki na duniya, Kpler, sun nuna cewa a watan Afrilu da Mayu, Indiya ta ƙara sayen mai daga Najeriya, Angola, Brazil da Venezuela domin cike gibin da ya biyo bayan matsalar Hormuz.
Rufe Hormuz: Indiya ta karkata ga Africa
A ruwayar jaridar Punch, Indiya da ke matsayi na uku a duniya wajen shigo da mai, ta dade tana dogaro sosai kan ƙasashen Gabas ta Tsakiya wajen samun makamashi kafin rikicin ya ƙara tsananta.
Mashigar Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya wajen safarar mai, domin dubunnan gangunan mai na ratsa yankin kullum zuwa sassa daban-daban na duniya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa duk da raguwar man da Indiya ke samu daga Rasha saboda gyaran wata matatar mai, har yanzu Rasha ce ke kan gaba wajen samar mata da mai, sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya.

Kara karanta wannan
NDC ta yi zargin wasu shugabanninta na karbar na goro domin tsayar da 'dan takara
Najeriya na cin gajiyar rufe Hormuz
Sai dai kuma Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka amfana da yunƙurin Indiya na faɗaɗa hanyoyin samun ɗanyen mai saboda rashin tabbas a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Facebook
Bayanan Kpler sun nuna cewa Indiya ta rage shigo da mai daga Rasha da kusan 29.4% idan aka kwatanta da watan Maris, 2026 inda adadin ya sauka zuwa kusan ganga miliyan 1.6 a rana.
A lokaci guda kuma, ƙasar ta ƙara shigo da mai daga UAE zuwa kusan ganga 669,700 a rana daga ganga 230,600 da aka samu a watan Maris, 2026.
Masana harkokin makamashi sun yi gargadin cewa duk wata doguwar tangarɗa da za ta hana zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz na iya jawo ƙarancin ɗanyen mai a duniya tare da tayar da farashin man fetur a ƙasashe masu shigo da shi.
Hormuz: Trump ya kuma magana kan sulhu
A baya, mun wallafa labarin cewa na ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran domin kawo karshen yakin da ake yi wanda ya faro tun daga ranar 28 ga watan Fabarairu, 2026.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa tattaunawa ta yi nisa domin cimma yarjejeniya a tsakaninsu kuma akwai alamun haske na cewa za a cimma yarjejeniya nan gaba kadan.
Sai dai Trump ya bayyana cewa mashigar Hormuz za ta kasance a bude nan ba da jimawa ba domin ci gaba da zirga-zirgar jiragen ruwa duk da yadda kasashen biyu suka ja daga game da sharadin kawo karshen yakin
Asali: Legit.ng
