Tsarabar Juma'a: Sunaye da hotunan masallatai 5 mafi kyau da girma a duniya
Masallaci dai wani tsarkakken wuri ne mai matukar daraja a wajen musulmai a dukkan fadin duniya musamman ma kasantuwar a cikin sa ne musulman suke samun natsuwa suyi munajati da mahaliccin su.
Kamar dai yadda musulunci da musulmai suka mamaye kusan dukkan lungu da sako a fadin duniyar nan, hakan ne ma ya sa suma masallatan suke da yawan gaske.
KU KARANTA: Yan damfara sun hadu da wasu mahajjata daga Arewa 8 a Madina
A duk inda musulmai dai suke da yawa, a bisa al'ada akan samu manya-manyan masallatai masu kyaun gaske inda sukan hadu domin yin ibadojin su.
Legit.ng dai ta tattaro maku wasu masallatan manya-manya kuma masu kyawun gaske:
1. Masallacin Haram – A garin Makka, kasar Saudiyya
2. Masallacin Annabi - A garin Madina, kasar Saudiyya
3. Masallacin Aqsa - a garin Jarusalam, kasar Falasdinu
4. Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddin – a kasar Brunei
5. Masallacin Zahir – A garin Kedah, kasar Malaysia
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng