Shugabar ALGON a Kano Ta Sha da Kyar bayan 'Yan Daba Sun Far Mata

Shugabar ALGON a Kano Ta Sha da Kyar bayan 'Yan Daba Sun Far Mata

  • Shugabar ALGON ta jihar Kano, Sa’adatu Maijama’a, ta tsallake rijiya da baya bayan harin da ake zargin ’yan daba sun kai mata a taron APC a Rano
  • Jami’an DSS sun kubutar da ita bayan wasu dauke da adduna sun yi yunkurin kai mata hari yayin da take kokarin shiga motar da gwamna Abba Kabir Yusuf ke ciki
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kira taron gaggawa kan matsalar tsaro da karuwar rikicin ’yan daba a Kano bayan an sau harin da rikicin daba a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Shugabar kungiyar ƙananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen jihar Kano, Sa’adatu Maijama’a, ta tsallake rijiya da baya.

Lamarin ya afku ne bayan harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai mata a yayin wani gangamin jam’iyyar APC da aka gudanar a garin Rano.

Kara karanta wannan

Borno: Yadda aka yi dauki ba dadi da yan ta'adda suka yi wa sojoji kwanton bauna

An kai wa shugabar karamar hukumar Tudun Wada hari
Kakakin raundunar yan sandan Kano Abdullahi Kiyawa, Hajiya Sa'adatu Maijama'a, shugabar ALGON a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa/Sa’adatu Salisu
Source: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa rahotanni sun bayyana cewa Sa’adatu Maijama’a, wacce ita ce shugabar karamar hukumar Tudun Wada ta sha da kyar da taimakon jami'an tsaro.

Kano: An kai wa shugabar ALGON hari

Rahotanni sun ce ta fuskanci harin ne lokacin da take kokarin karasawa wata motar bas kirar Coaster da ta dauko manyan jami’an gwamnati zuwa wajen taron, daga ciki har da gwamna Abba Kabir Yusuf.

Shaidun gani da ido sun ce wasu matasa dauke da adduna sun nufo ta tare da jifar abubuwa tare da kokarin kai mata hari kai tsaye.

Sai dai jami’an hukumar DSS da ke cikin tawagar gwamnan sun yi gaggawar shiga tsakaninsu, suka killace ta tare da saka ta cikin wata mota kirar SUV suka fice da ita daga wajen cikin hanzari.

Yadda aka kubutar da shugabar ALGON

Wani shaida ya ce ko bayan jami’an tsaron sun kubutar da ita, maharan sun ci gaba da farmakar motar da aka tafi da ita.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Matasa sun yi bore a Kano, sun kona wani ginin gwamnati

Jama'ian tsaron DSS sun samu nasarar ceto Hajiya Sa'adau
Shugabar ALGON ta jihar Kano, Hajiya Sa'adatu Maijama'a Hoto: Sa’adatu Salisu
Source: Facebook

Shaidan ya ce:

“Ba don saurin daukar matakin jami’an DSS ba, da lamarin zai iya zama sanadin rasa ranta."

Rahotanni sun kuma nuna cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya kira taron gaggawa na majalisar tsaro domin tattauna wannan lamari da kuma yadda rashin tsaro ke kara ta’azzara a wasu sassan jihar.

A kwanakin baya-bayan nan, mazauna Kano na ci gaba da nuna damuwa kan yadda hare-haren ’yan daba da rikice-rikicen siyasa suka yawaita a sassan jihar.

Rahotanni na cewa mutane da dama na rayuwa cikin fargaba sakamakon kashe-kashe da kuma jikkata mutane da makamai masu kaifi da ake samu kusan kullum.

A ranar 9 ga watan Mayu, kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta sanar da fara bincike kan karuwar tashe-tashen hankula da ayyukan ’yan daba masu alaka da siyasa a Kano.

Wasu matasan Kano sun yi bore

A baya, mun wallafa cewa wasu fusatattun matasa sun gudanar da zanga-zanga a jihar Kano domin jawo hankalin gwamnatin Abba Kabir Yusuf game da rashin tsaro a yankin Lakwaya.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a zaben fitar da gwani na APC, an tarwatsa masu kada kuri'a

Matasan sun fara zanga-zangar a matsayin ta lumana, amma daga baya lamarin ya rikide zuwa tashin hankali a Gwarzo, har aka kona wani sashe na ofishin karamar hukumar.

Zanga-zangar da suka yi ta biyo bayan karuwar ayyukan 'yan ta'adda da ake samu a Lakwaya da ke karamar hukumar Gwarzo inda aka kashe mutum biyu tare da sace wasu da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng