Ministan Iran Ya Je China, Kasashen 2 Sun Ragargaji Amurka tare
- Ministan harkokin wajen kasar China, Wanġ Yi, ya bayyana hare-haren soji da Amurka da Isra’ila ke kai wa Iran a matsayin abin da bai kamata ba
- Wanġ Yi ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da takwaransa na Iran, Abbas Araghchi, a birnin Beijing, kamar yadda rahotanni suka nuna
- A nasa bangaren, Ministan harkokin wajen Iran, Araghchi, ya gode wa China bisa tsayin daka da ta yi, musamman wajen yin Allah-wadai da Amurka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
China - Ministan harkokin wajen China, Wanġ Yi ya sake sukar yakin Amurka da Isra’ila a kan Iran, yana mai bayyana shi a matsayin haramtacce, tare da goyon bayan hanyoyin diflomasiyya domin kawo ƙarshen rikicin.
Rahotanni sun nuna cewa ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi a Beijing.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa ministocin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi dangantakar kasashen biyu, ciki har da haɗin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci, kafin su karkata ga batun halin da yankin ke ciki.
Maganar ministan harkokin wajen Iran
Araghchi ya bayyana China a matsayin ƙawa ta kusa kuma abokiyar hulɗa, yana mai jaddada kudirin Iran na ƙarfafa wannan haɗin gwiwa bisa girmama juna da amana.
Ya kuma yi bayani kan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a cikin kwanaki 40 na yaki, yana zarginsu da take dokokin jin ƙai na duniya, tare da gode wa China bisa matsayinta na kin amincewa da keta dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Yayin da China ke rike da shugabancin Majalisar Tsaro na wucin gadi, Araghchi ya bayyana fatan cewa rawar da Beijing za ta taka za ta taimaka wajen dakile ƙarin rashin bin doka.
Dangane da diflomasiyya, ya ce Iran na ci gaba da tattaunawa da Amurka ta hannun Pakistan, yana mai jaddada cewa duk da zama cikin shirin kare kanta, ƙasar na da niyyar ci gaba da bin hanyar sulhu.

Source: Getty Images
China ta soki kasar Amurka
Wanġ Yi ya yaba wa juriya da Iran ta nuna da kuma yadda take kokarin kauce wa ƙarin tashin hankali, yana mai jaddada goyon bayan China ga cikakken ikon ƙasar da tsaronta.
Ya ce matsayar China ita ce kin amincewa da amfani da karfi da kuma ci gaba da wannan yaki, yana mai cewa illolinsa sun wuce Iran zuwa sauran kasashe da al’ummomin duniya.
Merh News ta wallafa cewa kasashen sun yi nazari kan yarjejeniyoyin tattalin arziki da kasuwanci, inda suka amince da ci gaba da ganawa da tuntubar juna.
Amurka ta farmaki jirgin Iran
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin kasar Amurka sun kai hari kan wasu jiragen ruwan Iran da fararen hula ke tukawa a kusa da Hormuz.
Gwamnatin kasar Iran ta yi Allah wadai da harin, inda ta ce Amurka ta karya dokokin yaki da ta kai hari kan fararen hula a cikin ruwa.
Bayan tabbatar da kai harin, rundunar sojin kasar Iran ta bayyana cewa mutane biyar daga cikin wadanda da suke tuka jiragen sun mutu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

