Alaka za Ta Kare: Netanyahu Ya Tsara Raba Hanya da Amurka a Harkar Soji
- Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi wata doguwar hira game da yakin da ake da Iran da kuma makomar kasar shi game da karfin soji
- A bayanan da ya yi, Netanyahu ya bayyana cewa yana fatan kasar Isra'ila za ta daina dogaro da Amurka wajen karfin soja a shekaru masu zuwa
- Game da yaki da Iran, Firaministan Isra'ila ya bayyana cewa har yanzu ba za a ce an gama gwabzawa ba, ya ce akwai wasu abubuwa a kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Israel - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ce yana fatan ƙasarsa za ta daina dogaro da tallafin sojan Amurka cikin shekara 10 masu zuwa.
Ya bayyana haka ne a wata hira, inda ya ce Isra’ila na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙarta da ƙasashen yankin Gulf da ke kusa da ita a Gabas ta Tsakiya.

Source: UGC
Isra'ila za ta raba hanya da Amurka?
Benjamin Netanyahu ya yi magana kan daina dogaro da Amurka ne a wata hira da aka yi da shi a tashar CBS a ranar Lahadi, 10 ga Mayun 2026.
Ya ce:
“Ina son a rage tallafin kuɗi da Amurka ke ba mu gaba data, wato ɓangaren kuɗi na haɗin gwiwar soja da muke da shi,”
Ya ce Isra’ila na samun kusan dala biliyan 3.8 na tallafin soja daga Amurka a kowace shekara. Tun da farko Amurka ta amince za ta bai wa Isra’ila jimillar dala biliyan 38 na tallafin soja daga shekarar 2018 zuwa 2028.
Sai dai Netanyahu ya ce lokaci ya yi da ya dace su sake duba yiwuwar sake tsara alaƙar kuɗi tsakanin Amurka da Isra’ila ba tare da jinkiri ba.
“Ba na son jiran majalisa mai zuwa, ina son a fara aikin tun daga yanzu.”

Source: Getty Images
Maganar yakin Isra'ila da Iran
Netanyahu ya ce sai bayan fara yaƙi da Tehran ne masu tsara dabarun Isra’ila suka fahimci irin ƙarfin da Iran ke da shi wajen kawo karshen Mashihar Hormuz.
“An ɗauki lokaci kafin su fahimci girman wannan haɗari, wanda yanzu sun fahimta,”
In ji shi.
Sai dai Netanyahu ya ƙi yin bayani kan shirye-shiryen sojan Isra’ila a kan Iran, amma ya yi magana kan yiwuwar abin da zai faru idan aka samu sauyin shugabanci a Iran.
“Idan har wannan gwamnati ta raunana ko ma aka kifar da ita, ina ganin wannan shi ne ƙarshen Hezbollah, ƙarshen Hamas, kuma mai yiyuwa ƙarshen Houthis,”
In ji Netanyahu.
Shafin 60 Minutes ya wallafa bidyon Netanyahu a X:
An ba kasar Iran sirrin Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Isra'ila ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da tattara bayanan leken asiri domin ba kasar Iran.
Rahotanni da suka fito daga kasar sun nuna cewa uku daga cikin mutane hudun da ake zargi sojojin Isra'ila ne, daya kuma farar hula.
Gwamnatin kasar ta zargi mutanen da tattara bayanai da suka hada da hotunan wasu muhimman wuraren da suka hada da makarantun soji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

