Amurka Za Ta Jefa Iran a Sabuwar Matsala, Fada Ya Koma kan Gasar Cin Kofin Duniya

Amurka Za Ta Jefa Iran a Sabuwar Matsala, Fada Ya Koma kan Gasar Cin Kofin Duniya

  • Wani wakili na musamman na Shugaba Donald Trump ya buƙaci FIFA da ta cire Iran daga gasar cin kofin duniya, sannan ta maye gurbinta da Italiya
  • Wannan mataki na zuwa ne domin gyara dangantakar da ke tsakanin Trump da Firaministar Italiya, Giorgia Meloni, bayan takun-saƙa kan Fafaroma Leo XIV
  • Duk da cewa Italiya ba ta samu gurbin shiga gasar ba, Amurka ta ce tarihin ƙasar na lashe kofin sau huɗu ya isa dalilin da zai sa a shigar da su gasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka – Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta tura buƙata ta musamman zuwa ga hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) domin ganin an ba Italiya gurbin Iran a gasar cin kofin duniya mai zuwa.

Wakilin musamman na Amurka, Paolo Zampolli, ya tabbatar da cewa ya gabatar da wannan shawara ga Trump da kuma Shugaban FIFA, Gianni Infantino.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: ICIR ta fallasa 'boyayyun dalilan' Tinubu na tsige ministoci 2

Amurka ta fara makarkashiyar cire Iran daga gasar cin kofin duniya
Shugaban Amurka, Donald Trump (hagu) da Ministan wajen Iran, Abbas Araghchi (dama) Hoto: Anna Moneymaker / ATTA KENARE via Getty Images
Source: Getty Images

Amurka na son maye gurbin Iran da Italiya

A zantawarsa da jaridar Financial Times, Paolo Zampolli, ya bayyana cewa:

"Ni haifaffen Italiya ne, kuma zai kasance babban buri na ganin Italiya (Azzurri) a gasar da Amurka za ta karɓi baƙunci. Kasancewarsu masu kofuna huɗu, suna da darajar da za a iya sanya su a maimakon Iran."

Binciken jaridar ya nuna cewa wannan yunkuri wani salo ne na diflomasiyya domin sanyaya ran Firaministar Italiya, Giorgia Meloni.

Dangantakar shugabannin biyu ta yi tsami ne bayan da Trump ya fito fili ya soki Paparoma Leo XIV sakamakon matsayar da babban malamin addinin ya ɗauka kan yaƙin da ake yi da Iran.

Matsayar FIFA kan gasar cin kofin duniya

A watan Maris ne Italiya ta gaza samun gurbin shiga gasar a karo na uku a jere, sakamakon rashin nasara a bugun fanareti a hannun ƙasar Bosnia da Herzegovina.

A nata ɓangaren, hukumar ƙwallon ƙafa ta Iran (FFIRI) ta sanar a yau Laraba cewa tana nan tana shirye-shiryen tunkarar gasar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada sababbin ministoci 2 da ya fatattaki Wale Edun da Ahmed Dangiwa

Shugaban hukumar, Mehdi Taj, a ziyarar da ya kai birnin Tehran, ya bayyana cewa:

"A yanzu, shawarar da muke da ita ita ce tawagar ƙasar ta kasance cikin shiri tsaf domin gasar cin kofin duniya, muna kuma jiran umarni daga hukumomin ƙasar da abin ya shafa."
FIFA ta ce za ta ci gaba da gudanar da gasar cin kofin duniya yadda aka tsara.
Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino ya na daga hannu a filin kwallon kafa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Korafin Iran bai karbu a FIFA ba

Idan za a iya tunawa, Iran ta taɓa rokon FIFA da ta mayar da wasanninta ƙasar Mexico maimakon Amurka sakamakon yaƙin da ake yi, in ji rahoton The Guardian.

Sai dai tun a wancan lokacin, shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya jaddada cewa dukkan wasannin za su gudana ne kamar yadda aka tsara.

Ya zuwa yanzu, FIFA da kuma hukumar ƙwallon ƙafa ta Italiya (FIGC) ba su riga sun bayar da martani a hukumance kan wannan buƙata ta Amurka ba.

Trump ya magantu kan gasar cin kofin duniya

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa, Donald Trump, ya yi magana kan yiwuwar kasancewar Iran a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa ta shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗauki mataki kan buƙatar belin El Rufai, Malam zai zauna a hannun ICPC

Trump ya bayyana cewa bai damu ba idan tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar Iran za ta halarci gasar cin kofin duniya ta FIFA na 2026, a daidai lokacin da ake fuskantar rashin tabbas game da kasancewar kasar a gasar.

Tambayoyi sun taso game da kasancewar Iran a gasar sakamakon ƙaruwar rikici a Gabas Ta Tsakiya da kuma fargabar ko za a amince wa jami’an Iran da magoya bayansu su shiga Amurka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com