Iran Ta Lalata Jiragen Amurka bayan Kasar Ta Kai Mata Hari a Mashigar Hormuz
- Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta mayar da martani bayan kasar Amurka ta lalata mata wasu daga cikin jirangenta a yakin da ake yi
- Kasar ta harba makamai kan jiragen ruwan yakin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya wanda ke fama da yake-yake
- Rikici tsakanin Amurka da Iran na kara tsananta duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da kasashen Gulf suka fara fuskantar barazana
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Rahotanni sun bayyana cewa kasar Iran ta bude wuta kan wasu jiragen ruwan yakin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Hakan ya sanya sojojin Amurka suka mayar da martani tare da lalata wasu kananan jiragen ruwa shida na Iran.

Source: Facebook
Amurka ta dakile makaman linzami daga Iran
Shugaban rundunar CENTCOM ta Amurka, Admiral Brad Cooper, ya bayyana cewa sojojin Amurka sun dakile wasu makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki da Iran ta harba, cewar rahoton Al Jazeera.
Ya ce gwamnatin Donald Trump na kokarin taimaka wa jiragen ruwa su rika wucewa cikin mashigar Hormuz bayan rikicin ya hana zirga-zirga a yankin.
Cooper ya bayyana cewa ya gargadi Iran da kada ta kusanci kadarorin sojin Amurka yayin da Pentagon ke ci gaba da aiwatar da shirin “Project Freedom.”
Ya kara da cewa Amurka ta ci gaba da killace jiragen ruwa daga tashoshin jiragen Iran tare da girke jiragen yakin ruwa a Tekun Persian domin kare hanyoyin kasuwanci, cewar The Hill.

Source: Getty Images
Yawan jiragen ruwan da ke aiki a wurin
A cewarsa, jiragen ruwa daga kasashe 87 ne ke aiki a yankin, kuma Amurka na tattaunawa da kamfanonin jiragen ruwa domin tabbatar da ci gaba da zirga-zirga cikin kwanciyar hankali.
Ya bayyana cewa hakan ba zai taba rage kwazon sojojin Amurka ba yayin da ake ci gaba da yaki da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahoton ya ce wasu jiragen dakon kaya biyu sun samu tsallaka mashigar Hormuz karkashin kariyar jiragen yakin Amurka masu makamai masu linzami.
A gefe guda kuma, Iran ta kai wasu hare-hare kan kawancen Amurka a yankin Gulf, inda Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da cewa ta dakile wasu makamai masu linzami uku yayin da daya ya fada cikin teku.
Masu sa ido sun bayyana cewa rikicin tsakanin Amurka da Iran na kara kamari duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan da ya gabata.
Yakin da jawo matsaloli da dama musamman bayan rufe mashigar Hormuz wanda hakan ya taba tattalin arzikin duniya.
Iran ta gano karyar Amurka a yaki
Mun ba ku labarin cewa kasar Iran ta zargi Amurka da karya kan kudin da aka kashe yayin yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya a halin yanzu.
Jamhuriyar Musulunci da Isra'ila Iran ta ƙaryata wasu rahotanni kan asarar da Donald Trump ya yi tana cewa gwamnatinsa ta boye hakikanin adadin kuɗin.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce yakin ya jefa iyalan Amurka cikin karin kashe kudade, yana cewa kowane gida na biyan dala 500.
Asali: Legit.ng

