Trump Ya ‘Gano’ Raunin Iran a Yakin Isra’ila, Ya Bukaci Ta Mika Wuya

Trump Ya ‘Gano’ Raunin Iran a Yakin Isra’ila, Ya Bukaci Ta Mika Wuya

  • Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa kasar Iran ta rasa karfin sojoji sosai a yakin da ta ke yi da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya
  • Trump ya bukaci kasar ta mika wuya yana mai cewa kamata ya yi Tehran ta daga tutar zaman lafiya domin kawo karshen rikicin
  • Shugaban Amurka ya ce Iran na son cimma yarjejeniya a boye duk da kalaman barazana da take yi a bainar jama’a kan rikicin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana game da yakin da ake ci gaba da yi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Trump ya yi ikirarin cewa Iran ta rasa karfin soja sosai, yana mai cewa kamata ya yi kasar ta daga tutar mika wuya.

Amurka ta bukaci Iran ta mika wuya
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Donald Trump na Amurka. Hoto: Anadolu Ajansi, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Donald Trump ya kalubalanci karfin sojojin Iran

Kara karanta wannan

Abin da Trump ya ce kan tayin Iran na kawo karshen yaki da Amurka

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke White House ranar Talata 5 ga watan Mayun 2026, cewar Reuters.

Ya ce karfin sojin Iran ya ragu matuka, yana mai cewa abin da ya rage musu kawai shi ne amfani da kananan makamai marasa tasiri.

A cewarsa, duk da irin kalaman barazana da Tehran ke yi a bainar jama’a, a zahiri shugabannin Iran na son cimma yarjejeniya da Amurka.

Trump ya ce:

“Suna wasa ne kawai, amma gaskiyar magana ita ce suna son yarjejeniya saboda karfin sojinsu ya lalace.”

Ya kara da cewa idan wannan rikicin fada ne na gaske, da tuni Iran ta dakatar da duk wani yunkurin gaba.

Trump ya shawarci Iran ta yi gaggawar mika wuya
Shugaba Donald Trump a birnin New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Trump ya yaba da matakinsa kan Iran

Shugaban Amurkan ya kuma yabawa matakin killace tashoshin jiragen ruwan Iran da kasarsa ta dauka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya bayyana killacewar da cewa tana da karfi sosai kamar karfen da babu wanda zai iya karya shi ko kalubalantarsa.

Trump ya ce yana ganin matakin na aiki yadda ya kamata wajen matsa lamba kan Iran domin ta sauya matsayinta, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Sharadin Trump ga Iran yayin da ya ke shirin afkawa kasar da yaki karo na 2

Da aka tambaye shi abin da Iran za ta yi wanda zai karya yarjejeniyar tsagaita wuta, Trump ya ce lokaci zai nuna hakan.

Sai dai ya ce shugabannin Iran sun san abubuwan da bai kamata su aikata ba idan suna son kauce wa sabon rikici.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Amurka na ci gaba da bibiyar halin da ake ciki a yankin tare da nazarin matakai na gaba.

Trump ya jaddada cewa Iran ya kamata ta “ajiye farar tutar mika wuya” domin dakile ci gaba da tabarbarewar rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Amurka ta farmaki jiragen Iran

Mun ba ku labarin cewa rahotanni sun bayyana cewa sojojin kasar Amurka sun kai hari kan wasu jiragen ruwa da suka nufi Iran a kusa da mashigar Hormuz.

Gwamnatin Iran ta tabbatar da kai harin, inda ta ce an kashe wasu daga cikin fararen hula da ke cikin jirgin ba tare da sun aikata laifi ba.

Hakan na zuwa ne yayin da lamura ke kara zafi tsakanin Amurka da Iran a Gabas ta Tsakiya, musamman kan mashigar ruwan Hormuz.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.