Lamari zai Dagule: Iran Ta Ja Kunnen Trump game da Tura Sojoji Hormuz

Lamari zai Dagule: Iran Ta Ja Kunnen Trump game da Tura Sojoji Hormuz

  • Iran ta yi gargadin cewa za ta dauki duk wani yunkuri na Amurka na katsalandan a mashigar ruwan Hormuz a matsayin karya yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Hakan na zuwa ne yayin da shugaba Donald Trump ya ce sojojin Amurka za su fara rakiyar jiragen ruwa ta cikin mashigar Hormuz da kasar Iran ta toshe
  • Tattaunawa tsakanin kasashen biyu ta tsaya cak tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 8 ga Afrilun 2026, musamman kan Hormuz

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Gwamnatin kasar Iran ta yi martani yayin da shugaban Amurka ya yi maganar kawo shirin rakiyar jiragen ruwa da suka makale a mashigar Hormuz.

A wata sanarwa da shugaba Trump ya fitar, ya ce ya kawo shirin ne domin ceto wasu kasashe daga matsalar tattalin arziki duk da cewa bai bayyana sunan su ba.

Kara karanta wannan

A wata ga wata: Trump tunkari Iran da dakaru, zai tura sojoji Hormuz

Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei
Mojtaba Khamenei a Iran da wani jirgin yaki a gefen shi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadin Iran ga Amurka kan Hormuz

A wani sako da ya fitar a X, shugaban kwamitin tsaron kasa na majalisar dokokin Iran, Ebrahim Azizi, ya gargadi Amurka kan tsoma baki a mashigar Hormuz.

Ya bayyana cewa cewa duk wani katsalandan da Amurka za ta yi a tsarin zirga-zirgar ruwa a mashigar Hormuz za a dauke shi a matsayin karya yarjejeniyar tsagaita wuta.

Azizi ya kuma yi watsi da abin da ya kira wasan yara na Amurka, yana mai cewa ba za a tafiyar da mashigar Hormuz da Tekun Fasha ba da sakonnin Trump masu dauke da rudani.

Ya ce:

"Mashigar Hormuz da Tekun Fasha ba wurin maganganun siyasa ba ne.”
“Za mu dauki duk wani katsalandan din Amurka a sabon tsarin zirga-zirgar ruwan Hormuz a matsayin karya yarjejeniyar tsagaita wuta.!
Babu wanda zai yarda da wasan yara da Trump ke yi!”
Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump a wajen taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayanin masani kan Hormuz

Wani masani kan hadarin siyasar duniya, Marco Vicenzino ya shaida wa Al Jazeera cewa Amurka da Iran sun nuna ba su son komawa yaki da juna:

Kara karanta wannan

Iran ta yi magana, da yiwuwar yaki ya kuma barkewa tsakanin kasar Musulunci da Amurka

“Bangarorin biyu na gwada juna ne ba tare da son komawa yaki ba. Wannan wata hanya ce ta kokarin warware takaddamar da kuma samar da mafita, amma a lokaci guda akwai kuskuren fahimta,”

In ji shi.

Duk da haka, Marco Vicenzino ya bayyana cewa akwai yiwuwar sake yaki a tsakanin kasashen lura da abubuwan da ke cigaba da faruwa.

Ya jaddada cewa rikicin Iran da Amurka ba zai tsaya kan kasashen kadai ba, domin tasirin da zai iya yi wa kasuwancin duniya da zaman lafiya babba ne matuka.

An harbi jirgin ruwa a Hormuz

A wani labarin, kun ji cewa an budewa wani jirgin ruwan dakon kaya wuta yayin da ya yi yunkurin wucewa ta mashigar Hormuz da Iran ta toshe.

Rahotanni sun nuna cewa hukumar Birtaniya da ke kula da harkokin kasuwanci ta tabbatar da kai harin da kuma yin karin bayani.

Hakan na zuwa ne yayin da kasashen Iran da Amurka ke cigaba da takaddama kan yadda jirage za su rika wucewa ta mashigar Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng