Muhimman Abubuwa 5 da Suka Faru a Shirin Tattaunawar Iran da Amurka a Pakistan

Muhimman Abubuwa 5 da Suka Faru a Shirin Tattaunawar Iran da Amurka a Pakistan

Pakistan – Wakilan Amurka Steve Witkoff da Jared Kushner suna kan hanyar zuwa Pakistan domin halartar tattaunawar zaman lafiya kai-tsaye da ƙasar Iran, kamar yadda fadar White House ta bayyana.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya sauka a Pakistan tun da dadewa, amma Iran ta musanta cewa zai tattauna da Amurkawa.

Akwai yiwuwar tattaunawar Iran da Amurka ba za ta yiwu a makon nan ba
Dakin da aka gudanar da taron tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran a Pakistan. Hoto: Aamir QURESHI / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

A gefe guda kuma, Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta ci gaba da kai hari a Lebanon, inda ya ɗora wa ƙungiyar Hezbollah alhakin ƙoƙarin ruguza tsarin zaman lafiya, in ji rahoton CNN.

Ga wasu muhimman abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da batun sake tattaunawar Iran da Amurka a Pakistan:

1. Amurka ta ga "ɗan ci gaba" daga Iran

The Times of Israel ta rahoto sakatariyar yaɗa labarai ta fadar White House, Karoline Leavitt, ta bayyana cewa fadar White House ta "ga ɗan ci gaba" daga ɓangaren Iran a tattaunawar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Amurka za ta jefa Iran a sabuwar matsala, fada ya koma kan gasar cin kofin duniya

Dangane da sakamakon ziyarar Witkoff da Kushner, sakatariyar ta ce "Kowa zai kasance cikin shiri domin tashi zuwa Pakistan idan bukatar hakan ta taso."

2. Da wuya Ghalibaf ya halarci tattaunawar

Ba a sa ran Sshugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad-Bagher Ghalibaf, zai halarci tattaunawar kasarsa da Amurka a Pakistan, kamar yadda jami'an Amurka suka shaida wa CNN.

Jami'an fadar White House suna kallon Ghalibaf a matsayin shugaban tawagar Iran kuma takwaran mataimakin shugaban Amurka JD Vance.

3.Isra'ila da Hezbollah sun zargi juna

Dangane da abubuwan da ke faruwa a Lebanon, duka Isra'ila da Hezbollah sun zargi juna da karya yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta, in ji rahoton BBC.

Sharuɗɗan wannan yarjejeniya, wadda aka tsawaita ta na tsawon makonni uku bayan tattaunawa a Amurka, sun nuna cewa an yarje wa Isra'ila ta ɗauki "dukkan matakan da suka dace domin kare kanta."

4. IDF ta kashe mayakan Hezbollah

Shafin Arab News ya kuma rahoto dakarun tsaron Isra'ila (IDF) sun ce sun yi musayar wuta tare da kashe mayakan Hezbollah guda shida a garin Bint Jbeil da ke kudancin Lebanon a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Trump ya ci gaba da matsa lamba ga Iran, an fadi barnar da ya yi wa kasar Musulunci

Hakazalika, kafafen yaɗa labaran gwamnatin Lebanon sun ruwaito cewa dakarun IDF sun kashe mutane biyu a garin Touline.

An ce shugaban majalisar Iran ba zai halarci zaman tattaunawa da Amurka a makon nan ba.
Ministan Pakistan, Muhammad Shehbaz Sharif ya gana da Ministan wajen Iran Abbas Araghchi, Kakakin majalisa Mohammad Baqir Qalibaf da wasu wakilai a Islamabad. Hoto: Handout/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

5. Jami'in wanzar da zaman lafiya ya rasu

Wani jami’in wanzar da zaman lafiya ɗan ƙasar Indonesiya ya rasu bayan ya ji rauni a kudancin Lebanon a ƙarshen watan Maris, in ji rahoton Euro News.

Wannan ya ƙara yawan jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya (UNIFIL) da suka mutu zuwa shida tun lokacin da Isra'ila ta fara farmakin ta na soja a yankin.

Pakistan ta yi kaca-kaca da Isra'ila

A wani labari, mun ruwaito cewa, Ministan tsaron Pakistan, Khawaja Asif, ya bayyana Isra’ila a matsayin matsala ga bil’adama a cikin wani saƙo da ya fitar.

Khawaja Asif ya yi magana mai zafi game da Isra'ila, inda ya bayyana cewa yana fatan waɗanda suka kafa ta za su kasance cikin wadanda za a kona a lahira.

Rahoto ya nuna cewa kalaman Khawaja Asif, wadanda ya goge su, sun zo ne a lokacin da Islamabad ke ƙoƙarin taka rawar diflomasiyya domin dakile rikicin Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com