Ana tsaka da Maganar Sulhu, Trump Ya Yi Barazana Mai Ɗaga Hankali ga Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar ci gaba da kai hare-hare kan Iran ana maganar sulhu
- Trump ya yi wannan barazana ne idan har ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba cikin gaggawa
- Trump ya ce Iran na fuskantar matsin lamba sakamakon takunkumin jiragen ruwa da Amurka ta kafa a mashigar Hormuz wanda ya shafi fitar da mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC , US - Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin magana game da zaman tattaunawa a rikicin Iran.
Trump ya bayyana cewa zai ci gaba da kai hare-haren bama-bamai kan Iran idan har ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba cikin gaggawa.

Source: Getty Images
Trump ya sake barazana ga Iran
Rahoton New York Post ya ce Trump ya yi wannan barazana ne yayin da ake samun matsala game da zaman sulhu a tsakani.
Ya ce:
“Idan ba su son yarjejeniya, zan kammala ragowar kashi 25 cikin 100 na wuraren da muka sa a gaba ta hanyar soji."
Trump ya kuma sanar da tsawaita tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon makonni uku, yana mai cewa zai karbi bakuncin shugabanninsu a Fadar White House nan gaba.
Ya kare kansa daga tambayoyi kan tsawon lokacin yakin, yana mai cewa ya yi hasashen makonni hudu zuwa shida, kuma ya yi daidai saboda an lalata karfin sojin Iran.
Trump ya kara da cewa yakin ba zai dauki lokaci mai tsawo ba, yana mai cewa Iran na cikin rudani kuma tana kokarin tunkarar Amurka domin tattaunawa.
Ya ce Amurka na samun nasara dari bisa dari kan takunkumin jiragen ruwa a mashigar Hormuz, wanda ya janyo matsin lamba ga Iran sosai.
Rahotanni sun nuna shugabannin Iran na cikin damuwa saboda takunkumin, duk da cewa har yanzu ba su amince su shiga tattaunawa da Amurka ba.

Source: Twitter
Takaicin da Trump ya nuna kan farashin mai
Trump ya nuna takaici kan tambayoyi game da farashin mai, yana mai cewa hauhawar farashin na dan lokaci ne saboda rikicin da ake yi a yankin, cewar CNN.
Ya ce abin da Amurkawa za su samu shi ne Iran ba tare da makamin nukiliya ba, wanda zai hana yiwuwar kai hare-hare ga kasarsu ko yankin Gabas ta Tsakiya.
Trump ya yi watsi da tambayar ko zai yi amfani da makamin nukiliya, yana mai cewa bai dace a yi amfani da irin wannan makami ba ko da kuwa a irin wannan yanayi.
Ya jaddada cewa ba shi ne ke karkashin matsin lokaci ba, illa Iran, duk da cewa akwai wa’adin kwanaki 60 da majalisa ta gindaya kan ci gaba da yakin.
Trump ya cika baki kan mashigar Hormuz
Mun ba ku labarin cewa ana ci gaba da takaddama tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan mashigar ruwa ta Hormuz.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa sojojin ruwan kasarsa sun karbe iko da mashigar Hormuz wadda Iran ta kulle.
Donald Trump ya kuma bayyana tsawon lokacin da mashigar ta Hormuz za ta yi a karkashin ikon dakarun sojojin ruwan Amurka.
Asali: Legit.ng


