Jamus Ta Fadi Yadda Iran Ta ba Trump da Amurka Kunya yayin Gwabza Yaki

Jamus Ta Fadi Yadda Iran Ta ba Trump da Amurka Kunya yayin Gwabza Yaki

  • Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz ya yi maganganu game da yakin kwana 40 aka shafe ana yi tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila
  • A bayanin da ya yi, Friedrich Merz ya bayyana cewa shugabannin Iran da sojojinta sun ba Amurka kunya, yana cewa Donald Trump ya rasa mafita
  • Merz ya fadi haka ne yayin wani taro da aka yi a wata makaranta a Jamus domin wasu shirye-shirye da suka shafi cigaban tarayyar Turai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Germany - Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya ce Iran ta nuna karfi fiye da yadda Amurka ta zata a yakin da suka yi.

Rahotanni sun nuna cewa ya yi gargadin cewa rikicin na kara kamari ba tare da wata hanya bayyananniya ta kawo karshensa ba.

Kara karanta wannan

An tafka asara: Yadda Iran ta lalata manyan kadarorin Amurka a Gabas Ta Tsakiya

Friedrich Merz da Donald Trump
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz na tattaunawa da Donald Trump a White House. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jamus: "Iran ta kunyata kasar Amurka"

Rahoton DW ya nuna cewa Merz ya yi magana a ranar Litinin yana mai cewa shugabannin Iran na kan hanyar kunyata Amurka a wannan rikici da ke gudana.

Shugaban gwamnatin Jamus ya ce alamu sun nuna cewa Amurka ba ta da ingantaccen tsari game da yakin, tare da tambayar irin hanyar fita daga rikicin da take da shi.

“Iranawa sun nuna karfi fiye da yadda aka zata, sannan Amurkawa ba su da wata kwakkwarar dabara a tattaunawar da suke yi,”

In ji Merz yayin wata ziyara da ya kai wata makaranta a Marsberg, wani gari a yankin Sauerland.

Ya kara da cewa matsalar irin wadannan rikice-rikice ita ce ba wai shiga kawai ake yi ba, dole ne a san yadda za a fita. Ya ce an ga irin wannan matsala a Afghanistan na tsawon shekaru 20, haka kuma a Iraki.

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya kuma sako magana, kasar Iran ta gabatar da sabon tayi ga Amurka

“A halin yanzu, ban ga irin hanyar fita da Amurka za ta bi ba, musamman ganin yadda Iran ke sarrafa tattaunawar da kwarewa — ko ma yadda take kauce wa tattaunawa cikin dabara,”

In ji shi.

Merz ya kara da cewa:

“Kasar Amurka gaba daya na fuskantar shan kunya daga jagorancin Iran, musamman daga rundunar IRGC.”

Yadda rikicin Iran ke shafar Jamus

Rahoton Yahoo News ya nuna cewa Merz ya ce wannan yanayi mai sarkakiya a Gabas ta Tsakiya na haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin Jamus.

“A yanzu lamarin ya rikice sosai,”
“Kuma yana jawo mana asarar kudi mai yawa. Wannan rikici na da tasiri kai tsaye kan yawan abin da muke samarwa a bangaren tattalin arziki.”

In ji shi.

Wasu sojojin Amurka da Iran ta kashe
Sojojin Amurka da Iran ta kashe a Gabas ta Tsakiya. Hoto: @HouseGOP
Source: Twitter

Ya kuma bayyana cewa Jamus na ci gaba da shirinta na tura jiragen share nakiyoyi domin taimakawa wajen bude mashigar ruwa ta Hormuz, inda kaso mai yawa na man fetur na duniya ke bi.

Manufar Amurka kan NATO

A wani labarin, kun ji cewa an samu wani sakon imel da ke nuna irin shirin da Gwamnatin shugaba Donald Trump ke yi wa kasashen NATO

Kara karanta wannan

An tono shirin da Amurka ta yi wa Spain da kasashen da suka ki taya ta yakar Iran

A sakon, Amurka ta tsara wasu matakai da za ta dauka kan kasashen da suka ki taimaka mata yayin da take gwabza fada da Iran.

An ce daga cikin matakan da Trump ke son dauka akwai dakatar da Spain da ta hana shi amfani da filin jirgin samanta a lokacin yakin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng