Yaƙi Zai Ci Isra'ila har Gida, Ta Gano Dakarun da ke Yi wa Iran Leƙen Asiri
- Kasar Isra’ila ta gurfanar da jami’an rundunar sojin sama biyu kan zargin suna yi wa jamhuriyar Musulunci ta Iran aiki
- Ana tuhumar su da taimaka wa 'maƙiya' da yada bayanan sirri masu matuƙar muhimmanci
- Isra'ila na wannan zarge-zargen yayin da ake ci gaba da yakin da ita da Amurka suka fara ta hanyar kai wa Iran hari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Israel – Gwamnatin Isra’ila ta gurfanar da wasu jami’an rundunar sojin sama guda biyu a gaban kotu bisa zargin yin aiki da hukumomin leƙen asirin Iran.
Rahotonni sun nuna cewa an kama mutanen biyu ne bayan bincike mai zurfi da hukumomin tsaron cikin gida da na soja suka gudanar.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa wannan na cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ila ta fitar tare da haɗin gwiwar hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet da kuma ‘yan sanda.
Isra'ila na zargin jami'anta da leken asiri
Times of Israel ta ruwaito mutanen biyun, waɗanda ke aiki a matsayin masu gyaran kayan aiki, na fuskantar tuhume-tuhume masu tsanani da suka haɗa da taimaka wa maƙiya da kuma yada bayanan sirri.
Hukumomin tsaro sun bayyana cewa irin waɗannan laifuffuka na barazana kai tsaye ga tsaron ƙasar mai yaki da mawkabtan ƙasashe.
Sanarwar ta ƙara da cewa an tuhumi ɗaya daga cikin sojojn da yin hulɗa kai tsaye da wakilin wata ƙasa waje, yayin da ɗayan kuma ake zargin ya taimaka wajen sauƙaƙa wannan hulɗa. .
Wannan lamari ya jawo hankalin jama’a, musamman duba da irin mahimmancin rundunar sojin sama a tsarin tsaron Isra’ila.
Ana zargin sojan Isra'ila da taimakon Iran
Hukumomin tsaro sun ce a yayin bincike, mutanen biyun sun bayyana cewa da farko sun yanke hulɗa da mutanen Iran bayan sun ƙi aiwatar da wasu ayyuka da suka shafi makamai.
Duk da haka, daga baya ana zargin sun sake yunƙurin komawa hulɗa da su bayan an katse sadarwa daga ɓangaren Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kara karanta wannan
Hankalin iyalan mutum 416 da Boko Haram ta sace ya tashi yayin da wa'adi ya kusa cika
Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta bayyana cewa ɗaya daga cikin sojojin ya aika wa wani wakilin Iran da wasu muhimman bayanai na horon soja da suka shafi tsarin jiragen yaƙi.

Source: Facebook
Haka kuma, ana zargin ya miƙa bidiyo da hotunan wasu wurare da ke cikin sansanin soja, daga ciki har da wuraren da ake gudanar da ayyuka masu matuƙar sirri.
Masu sharhi kan harkokin tsaro sun bayyana cewa irin wannan zargi na iya yin tasiri mai girma ga tsaron Isra’ila, musamman idan aka tabbatar da cewa bayanan da aka fitar sun kai hannun ƙasar da ake kallon abokiyar gaba.
Har yanzu dai ana ci gaba da shari’ar, yayin da hukumomi ke ƙoƙarin gano ko akwai wasu da ke da hannu a cikin wannan al’amari.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Isra’ila da Iran ke ƙara tsananta, lamarin da ke sa duk wani zargi na leƙen asiri ya zama mai matuƙar muhimmanci a fagen tsaro da siyasa.
An kai wa tsohon ɗan sarkin Iran hari
A baya, kun ji cewa dan tsohon sarkin Iran da aka kifar da gwamnatinsa a 1979, Reza Pahlavi ya gamu da wani mummunan lamari yayin da ya je taro a Jamus.
Wani mutum ya kutsa wajen da Reza Pahlavi ke tafiya ya fesa masa ruwan tumatur a wuya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin duniya baki daya.
Reza Pahlavi ya sha nuna kan shi a matsayin wanda ya kamata a ce yana mulkin Iran a yanzu kuma yana goyon bayan hare-haren Amurka a kan ƙasarsa.
Asali: Legit.ng

