Iran Ta Saki Bidiyon Yadda Sojojinta Suka Kwace Jiragen Ruwa a Hormuz

Iran Ta Saki Bidiyon Yadda Sojojinta Suka Kwace Jiragen Ruwa a Hormuz

  • Ana cigaba da takaddama tsakanin Iran da Amurka game da iko da mashigar Hormuz da kuma tekun Oman da Donald Trump ya ajiye sojoji
  • Rundunar sojin Iran ta fitar da bidiyon yadda sojojinta suka kama wani jirgin ruwa suka tafi da shi duk da barazanar da Trump ke mata
  • Fadar White House ta fitar da sanarwa game da kwace jiragen da Iran ta ce ta yi, inda ta yi magana kan tsagaita wuta da Trump ya sanar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Iran da Amurka na cigaba da caccaka tsinke a Gabas ta Tsakiya duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaba Donald Trump ya sanar.

Iran ta cigaba da farautar jiragen ruwan da suke yunkurin wucewa ta mashigar Hormuz bayan rufe shi da ta yi a karshen makon da ya wuce.

Kara karanta wannan

Hormuz: Ana zargin dakarun Iran sun buɗe wa jirgin ruwan da ya yi kunnen ƙashi wuta

Jirgin ruwan Iran na tafiya a teku
Wani jirgin ruwa dauke da tutar Iran a teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bidiyon da Iran ta fitar a Hormuz

Reuter ta rahoto cewa rundunar juyin juya halin Iran ta fitar da wani bidiyo da ya nuna yadda sojojinta suka kama wani jirgin ruwa a mashigar Hormuz.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin ɗaukar kayan na daga cikin jirage biyu da Iran ta kama a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilun 2026.

Iran ta ce jiragen suna aiki ba tare da izinin dakarun sojinta ba, kuma sun yin katsalandan ga tsarin tafiya na jiragen ruwa a Hormuz.

A bidiyon da Al Jazeera ta wallafa a X, an hango sojojin Iran na fitowa a cikin jirginsu suna karkatar da jirgin ruwan:

Martanin Trump kan kwace jiragen

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce kama jiragen da Iran ta yi a mashigar Hormuz bai karya yarjejeniyar tsagaita wuta, domin ba jiragen Amurka ko na Isra’ila ba ne.

Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta nuna hakan ba abin damuwa ba ne, yayin da sojojin Amurka ke ci gaba da kakaba takunkumin ruwa a daidai lokacin da tashin hankali ke karuwa.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta gindaya sharuɗan sake zama a teburin tattaunawa da Amurka

Fadar White House ta bayyana cewa Trump ba ya kallon kama jiragen da Iran ta yi a matsayin abin da zai karya yarjejeniyar tsagaita wuta.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Donald Trump yana sauraron bayani a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Leavitt ta ce an “wuce gona da iri” wajen yada labarin, tana mai cewa jiragen ba na Isra’ila ba ne, don haka Iran ba ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ba.

Wannan na zuwa ne makonni bayan Trump ya yi barazanar cewa idan Iran ta harba makami kan wani jirgin ruwa a Hormuz, za a murkushe ta gaba daya.

An kori babban sojin Amurka

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin shugaba Donald Trump ta kasar Amurka ta sanar da korar shugaban rundunar sojin ruwa, John Phelan a ranar Laraba.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da takaddama tsakanin Amurka da Iran a teku a Gabas ta Tsakiya, inda ake tsammanin sojojin ruwa za su taka rawa sosai.

Gwamnatin Trump bata bayyana hakikanin dalilan sauke John Phelan ba, sai dai an ce ya cika samun sabani da ministan yakin kasar kan sarrafa jiragen ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng