"Ta Yaudare Mu Sau 2," Iran Ta Sake Tona Asirin Amurka ana Shirin Komawa Teburin Sulhu
- Har yanzu kasar Iran ba ta yanke shawarar ko za ta halarci zagaye na biyu na zaman tattaunawar sulhu da Amurka a kasar Pakistan ba
- Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei ya ve kasarsa ba za ta manta da yaudara biyu da Amurka ta mata ba
- Ya kuma zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta tun daga batun Lebanon, da kuma rufe tashohin ruwan Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Iran ta bayyana cewa har yanzu ba ta yanke shawarar ko za ta shiga zagaye na biyu na tattaunawa da Amurka ba, duk da kasar Pakistan da ke shiga tsakani, ta kammala shirye-shirye.
Kasar musulunci ta Iran ta tuna yadda Amurka ta kai mata hare-hare a daidai lokacin da ake tsaka da tattaunawar diflomasiyya, tana mai cewa ba za ta taba manta wa da hakan ba.

Kara karanta wannan
Bayan ta kekashe kasa, Amurka ta gabatar da sabon tayi ga kasar Musulunci ta Iran

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa Iran ta zargi Washington da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma rashin nuna gaskiya a harkokin diflomasiyya.
Iran ba ta shirya komawa sulhu ba
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Esmaeil Baghaei, ne ya bayyana hakan yau Litinin, 20 ga watan Afrilun 2026, ya ce Iran ba ta da wani shiri a yanzu na gudanar da tattaunawa ta gaba.
"A daidai lokacin da nake muku magana yanzu, ba mu da wani shiri na halartar zagaye na gaba na tattaunawa," in ji shi.
Baghaei ya bayyana cewa Washington ta dakile shirin ci gaba da zaman sulhu tun daga farkon tsagaita bude wutar saboda ci gaba da kai hare-hare Lebanon da Isra'ila ta yi.
Iran ta zargi Amurka da karya alkawari
Ya ce Amurka ta fara kokarin kafa hujjar cewa Lebanon ba ta cikin yarjejeniyar, duk kuwa da cewa mai shiga tsakani watau Pakistan ta bayyana akasin haka.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Kasar Musulunci ta Iran ta jikawa Amurka aiki ana shirin komawa teburin sulhu
A cewarsa, Amurka ta ci gaba da abin da Iran ta kira killace hanyoyin ruwa da sauran ayyukan kiyayya a ciki da kewayen mashigar Hormuz, ciki har da harin da aka kai wa wani jirgin ruwan kasuwanci na Iran.
Ya ce irin wadannan ayyuka keta yarjejeniyar tsagaita wuta ne a sarari, kuma rufe hanyoyin ruwan kansa ya zama wani mataki na cin zarafi a karkashin dokokin kasa da kasa.

Source: Getty Images
Yaudarar Amurka da Iran ba za ta manta ba
Haka kuma, Baghaei ya bayyana cewa Tehran ba za ta manta da abin da ya kira yaudarar diflomasiyya har sau biyu da Amurka ta yi a cikin shekarar da ta gabata ba.
Ya ce kasar Amurka ta kai wa Iran hari har sau biyu yayin da ake tsaka da tattaunawar diflomasiyya, kamar yadda kafar yada labarai ta Iran International ta ruwaito.
"Ba za mu iya mantawa da cewa Amurka ta ci amanar diflomasiyya har sau biyu ba," in ji shi.
Iran ta fara gyara makamanta
A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta fara kera sababbin makamanta da harsasai a lokacin tsagaita wuta da aka cimma da Amurka da taimakon Pakistan.

Kara karanta wannan
Lissafi ya canza, Iran ta tura sako 'mara dadi' zuwa Amurka kan batun zaman sulhu
Kwamandan rundunar sararin samaniya ta dakarun IRGC ta kasar Iran, Brigediya Janar Seyed Majid Mousavi, ne ya tabbatar da hakan.
Ya ce kasar ta gyara na’urorin harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da suka samu matsala a yayin yakin da ta yi da Amurka da Isra'ila.
Asali: Legit.ng