Iran Ta Kafe kan Sharadin Sulhu da Amurka, Ta Yi Fatali da Tsagaita Wuta na Wucin Gadi

Iran Ta Kafe kan Sharadin Sulhu da Amurka, Ta Yi Fatali da Tsagaita Wuta na Wucin Gadi

  • Iran ta ce ba za ta amince da tsagaita wuta na dan lokaci ba yayin da Amurka da Isra'ila ke hararar ƙasashen shiyyar
  • Tana wannan batu ne jim kadan bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ana dab da cimma matsaya
  • Iran ta zargi Amurka da Isra’ila da haddasa rashin zaman lafiya a yankin Iran ta dage kan kawo karshen yaki gaba daya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran –Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, ya bayyana cewa kasarsa ba za ta amince da duk wani tsagaita wuta na wucin gadi ba.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta karya yarjejeniya a Lebanon, ta kai munanan hare hare bayan jawabin Trump

Saeed Khatibzadeh ya bayyana cewa Iran na son a kawo karshen yakin gaba daya a yankin Gabas ta Tsakiya da ake kai wa hari ɗaya bayan ɗaya.

Iran ta ce ba za ta lamunci sulhun wurin gadi ba
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: KhameneiIT/x
Source: Twitter

Al-Jazeera ta wallafa cewa Khatibzadeh ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a wani taro, inda ya jaddada cewa duk wata yarjejeniyar tsagaita wuta dole ta shafi dukkannin wuraren rikici a yankin.

Iran ta magantu kan sulhu da Amurka

Anadolu Ajansi ta ruwaito cewa Saeed Khatibzadeh ya ce dole ne a hada dukkannin yankunan da ake fama da rikici “daga Lebanon zuwa Tekun Maliya”, yana mai cewa wannan batu shi ne jan layi ga Iran wanda ba za ta yi wasa da shi ba.

Khatibzadeh ya kara da cewa:

“Ba za mu amincewa da tsagaita wuta na wucin gadi ba."

Mataimakin Ministan ya jaddada cewa ya kamata a kawo karshen wannan jerin rikice-rikicen gaba daya sau daya tak, ba tare da sake dawowa kansu ba.

Kara karanta wannan

Iran ta amince da bukatar Amurka, ta canza shawara kan batun kera makamin nukiliya

Matsayar Iran kan yaƙin Gabas ta Tsakiya

Saeed Khatibzadeh ya ce wannan matsaya na Iran na nuna bukatar samun zaman lafiya mai dorewa, ba wai dakatar da fada na dan lokaci ba, wanda zai iya sake barkewa a nan gaba.

Iran ta zargi Isra'ila da Amurka da jefa Gabas ta Tsakiya a matsala
Benjamin Netanyahu tare da Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: UGC

A bangare guda, jami’in na Iran ya zargi Amurka da Isra’ila da haddasa rashin zaman lafiya a yankin, yana mai cewa matakan da kasashen biyu ke dauka sun kara dagula lamura.

Ya ce wadannan ayyuka sun yi mummunar illa ga harkokin kasuwanci na duniya da kuma tattalin arziki baki daya, musamman ganin muhimmancin yankin wajen jigilar kayayyaki.

Dangane da mashigar ruwa ta Hormuz, Khatibzadeh ya ce duk da kasancewarta karkashin ikon Iran, mashigar ta dade tana bai wa kasashen duniya damar wucewa cikin sauki.

Ya nuna cewa Iran na da niyyar ganin an kawo karshen rikice-rikice a yankin baki daya, tare da samar da zaman lafiya mai dorewa da zai amfani kowa.

Kara karanta wannan

Trump ya sanar da matsayar da Israila da Lebanon suka cimma kan tsagaita wuta

Amurka ya magantu kan yakin Iran

A baya, mun wallafa cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazana da cewa karfin sojin ƙasarsa shi ne mafi girma a dukkanin faɗin duniya.

Donald Trump ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke bayyana cewa yakin da ƙasarsa ke yi da Iran na tafiya cikin sauƙi tare da burgar cewa sun fi kowa ƙarfin soja.

Ana sa ran sabon zagayen tattaunawa tsakanin Amurka da Iran nan gaba kaɗan, inda ake ganin Trump zai iya zuwa da kansa domin kawo ƙarshen yaƙin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng