Abin Mamaki: Amurka Ta Taimaki Kasar Musulunci Ta Iran, Ta Yi Abin Alheri a Hormuz
- A karon farko bayan tsagaita wuta, Amurka ta taimaka wa Iran wajen kakkabe yan fashin teku a mashigar ruwa ta Hormuz
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ne ya bayyana hakan yayin da yake martani kan sanarwar bude mashigar da Iran ta yi yau Juma'a
- Trump ya kuma bayyana cewa ya yi fatali da tayin kungiyar tsaro ta NATO, wacce ta nemi izinin kawo dauki don tabbatar da tsaron Hormuz
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Amurka ta bayyana cewa ta kai dauki tare da taimaka wa kasar Musulunci ta Iran wajen kakkabe yan fashin teku da duk wani abu da ka iya zama matsala a mashigar ruwa ta Hormuz.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ne ya bayyana hakan yau Juma'a, 17 ga watan Afrilu, 2026 yayin da yake jawabi bayan bude mashigar ruwan da Iran ta yi.

Source: Getty Images
Iran ta bude mashigar ruwa ta Hormuz
Tun farko dai rahoton tashar Al-Jazeera ya tabbatar da cewa Iran ta ayyana bude mashigar Hormuz ga kowane jirgin ruwa sakamakon tsagaita wuta a kasar Lebanon.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce mashigar za ta ci gaba da aiki bisa ka'idoji da tsare-tsaren da rundunar sojin kasar ta shimfida.
Sai dai wani babban jami’in soja na Iran ya shaida cewa duk jiragen ruwa da ke son wucewa ta mashigar Hormuz dole ne su samu izini daga rundunar juyin juya hali watau IRGC.
Haka kuma, wani jami’i ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an amince duk jiragen kasuwanci su ratsa mashigar, har da na Amurka, amma ba za a bari jiragen yaki su bi ta wannan hanya ba.
Taimakon da Amurka ta yi wa Iran
Da yake karin bayani kan bude mashigar, Trump ya kara da cewa Iran, tare da taimakon Amurka, na ci gaba da kakkabe duka yan fashin ruwa da nakiyoyin da aka dasa a mashigar.

Kara karanta wannan
Iran ta kafe kan sharadin sulhu da Amurka, ta yi fatali da tsagaita wuta na wucin gadi
Sai dai babu wata sahihiyar shaida daga bangaren Iran da ta tabbatar da wannan batu da Trump ya yi har kawo yanzu.

Source: Getty Images
Donald Trump ya yi fatali da taimakon NATO
Trump ya kuma yi ikirarin cewa kungiyar NATO ta tuntube shi domin taimakawa wajen tsaron mashigar, amma ya ce ya ki amincewa, yana mai cewa su “su nisanta kansu” daga lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa yarjejeniyar tsagaita wuta na samun ci gaba ne a hankali a hamkali, inda ake danganta zaman lafiya a Lebanon da bude mashigar Hormuz.
Wannan dai na zuwa ne yayin da kasashen biyu ke kokarin sake komawa teburin tattaunawa domin cimma yarjajeniyar zaman lafiya ta karshe.
Trump ya nuna alamun sulhu da Iran
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya nuna yiwuwar sake gudanar da tattaunawa kai tsaye tsakanin jami’an Amurka da na Iran.
Wannan dai na zuwa ne yayin da Pakistan ke ci gaba da kokarin dawo da bangarorin biyu zuwa teburin tattaunawa bayan tashi taron farko ba tare da cimma matsaya ba.
Shugaba Trump ya ce alamu sun nuna Amurka da Iran za su fahimci juna kuma wannan yaki zai kare nan ba da dadewa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
