Babbar Bukatar da Amurka Ta Gabatarwa Iran yayin Tattaunawa a Pakistan
- Amurka da Iran sun zauna a teburin tattaunawa domin cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
- Tawagar Amurka ta mika bukatarta ga takwararta ta Iran kan batun inganta sinadarin Uranium da ake takaddama a kai
- Iran ta ki yarda da abin da Amurka ta gabatar, inda ta bayyana abin da take ganin za ta iya yi dangane da lamarin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Amurka ta mika bukata ga Iran yayin tattaunawar da aka yi a kasar Pakistan.
Amurka ta buƙaci ƙasar Iran da ta amince da dakatar da inganta sinadarin Uranium na tsawon shekaru 20 yayin tattaunawar da aka yi a birnin Islamabad a ƙarshen mako.

Source: Twitter
Tashar Axios ta ce wani jami’in Amurka da wata majiya mai masaniya kan lamarin suka sanar mata da hakan.

Kara karanta wannan
Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad
Martanin kasar Iran ga Amurka
A cewar majiyoyin Iran ta mayar da martani da cewa ba za ta iya wuce shekaru waɗanda ba su kai 10 ba.
Sabani kan shirin nukiliyar Iran musamman kan ko Tehran za ta amince ta daina inganta uranium da kuma miƙa dukkan abin da take da shi a ajiye, shi ne babban abin da ya kawo cikas ga cimma yarjejeniyar.
Ana ci gaba da yunkurin cimma yarjejeniya
A halin yanzu, masu shiga tsakani daga ƙasashen Pakistan, Masar, da Turkiyya suna ƙoƙarin dinke ɓarakar da ke tsakani domin cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin kafin yarjejeniyar tsagaita wutar da ake kai ta ƙare a ranar 21 ga Afrilun 2026.
A gefe guda kuma, Shugaba Trump ya sanar da killace hanyoyin ruwan Iran a matsayin wani mataki na ƙara matsin lamba domin ya samu galaba a tattaunawar.
"Akwai ci gaba da tuntuɓar juna tsakanin Amurka da Iran kuma ana samun ci gaba zuwa ga cimma yarjejeniya."
- Wani jami'in Amurka
Trump ya shaida wa manema labarai a fadar White House ranar Litinin, 13 ga watan Afirilun 2026 da yamma cewa:
"Wasu mutanen da suka dace a Iran sun kira mu a safiyar nan... kuma suna son ƙulla yarjejeniya."
Abubuwan da suka faru a sirrance
Amurka mai karfin tattalin arziki da soja ta buƙaci aƙalla shekaru 20 na dakatar da inganta Uranium tare da wasu tsauraran sharuɗɗa.
Hakazalika, Amurka ta buƙaci Iran ta fitar da dukkan uranium ɗin da ta riga ta inganta zuwa daga ƙasar.
Iran ta ƙi yarda, inda ta ce za ta amince ne kawai a rage ƙarfin sinadarin a cikin ƙasar ƙarƙashin sa ido.
Ba a cimma yarjejeniya a zaman farko ba
Majiyoyi sun ce jami'an Iran sun yi tsammanin sun kusa cimma yarjejeniyar farko a safiyar Lahadi, amma sai kalaman mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, suka ba su mamaki, jaridar The Times of Israel ta kawo rahoton.

Source: Twitter
Vance ya bayyana cewa babu wata yarjejeniya da ke kusa, sannan ya ɗora wa Iran laifi kuma ya sanar da cewa tawagar Amurka za ta bar Islamabad.
"Iran ta yi fushi sosai da wannan taron manema labarai na Vance."
- Wata ata majiya
Wani mamba a Majalisar dokokin Iran da ke cikin tawagar tattaunawar, Seyyed Mahmoud Nabavian, ya tabbatar a ranar Litinin cewa buƙatun Amurka guda biyu kan batun nukiliya ne suka hana cimma yarjejeniyar.
Trump ya yi barazana ga Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Donald Trump ya yi gargadin latata duk wani jirgin ruwan yakin Iran da ya tunkari shingen da ya kafa don killace tashoshin jiragen ruwan kasar.
Shugaban na Amurka ya bayyana cewa an riga an ruguza yawancin dakarun ruwan Iran a lokacin yaƙin.
Asali: Legit.ng
