Kudurin Hana Trump Sayar wa Isra'ila Bama Bamai Ya Gamu da Cikas a Majalisar Dattawa
- Majalisar dattawan Amurka ta yi watsi da ƙudirin dakatar da sayar da makamai na kusan Dala miliyan 500 ga Isra’ila
- Sanata Bernie Sanders ya jagoranci yunƙurin, amma bai samu rinjayen da zai sa hakansa ya cimma ruwa ba
- Sama da Dala biliyan 21 Amurka ta bai wa Isra’ila tun bayan fara yaƙin Gaza a 2023 inda ta ke kai harin ƙare dangi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
USA – Majalisar dattawan Amurka ta ƙi amincewa da wasu kudurori guda biyu da aka gabatar domin dakatar da sayar da makamai ga Isra’ila, kimanin Dala miliyan 500.
Wadannan kudurori sun fito ne daga Sanata Bernie Sanders, wanda ke wakiltar jihar Vermont kuma mai zaman kansa ne amma yana aiki tare da jam’iyyar Democrat.

Source: Facebook
TRT World ta wallafa cewa a kuri’ar da aka kada ranar Laraba 15 ga watan Afrilu 2026, majalisar ta ƙi dakatar da sayar da buldoza masu sulke na Dala miliyan 295, inda aka kada kuri’a 40 na goyon baya da 59 na adawa.
An samu sabani a Majalisar Amurka
Reuters ta wallafa cewa wasu sanatocin Democrat daga ciki har da Chuck Schumer sun hade da ‘yan Republican wajen kin amincewa da kudirin sanya wa Amurka takunkumi.
Haka zalika, wani kudiri na biyu da ke neman hana sayar da bama-bamai masu nauyin fam 1,000 na Dala miliyan 151.8 shi ma bai kai ga nasara ba
Wannan mataki na nufin Amurka za ta ci gaba da shirin sayar da wadannan makamai ga gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu.
Yadda Amurka ke tallafa wa Isra'ila
Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta bayar da tallafin soja sama da Dala biliyan 21 ga Isra’ila tun watan Oktoba na shekarar 2023, lokacin da rikicin Gaza ya tsananta.
Duk da rashin nasarar kudirin, Sanders ya nuna cewa akwai karuwar adawa a cikin majalisar, musamman daga ‘yan Democrat kan alakar sayar da makaman.
Ya ce a baya mutane 11 ne kacal suka goyi bayan irin wannan mataki, amma yanzu kusan sanatoci 40 daga cikin 47 na jam’iyyar Democrat sun nuna adawa da sayar da buldozar.

Source: UGC
Sanders ya danganta wannan sauyi da ra’ayin jama’ar Amurka, yana mai cewa bincike ya nuna 60% na Amurkawa na adawa da aika makamai zuwa Isra’ila, daga ciki har da mafi yawan ‘yan Democrat.
Ya kuma jaddada cewa wadannan buldoza ana amfani da su wajen rusa gidajen Falasdinawa a yankunan West Bank da Gaza, abin da ya ce yana hana yiwuwar kafa kasar Falasdinu.
Sanders ya soki manufofin Isra’ila, yana cewa Amurkawa ba su son kudinsu ya taimaka wajen abin da ya kira yaƙin fadada iko da ke cike da take hakkin bil’adama.
An shirin hana sayar da makaman Amurka
A baya, kun ji cewa ana ci gaba da samun masu fada a ji a Amurka na nuna adawa game da alakar kasar da Isra'ila kan sayar wa Tel Avi makamai da sauransu.
Rahotanni sun nuna cewa Sanata Bernie Sanders ya yi alƙawarin tilasta dakatar da sayar da makaman Amurka ga Isra’ila a majalsar kasar idan an kuma zama.
Bernie Sanders ya kasance na gaba-gaba wajen caccakar yake-yake da Donald Trump ke yi da kuma hare-haren Isra'ila a Gaza da Lebanon da ke raba Mutane da rayukansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


