Jerin Ƙasashen da Ke tare da Iran da Waɗanda Ke Goyon bayan Isra'ila da Alaƙarsu

Jerin Ƙasashen da Ke tare da Iran da Waɗanda Ke Goyon bayan Isra'ila da Alaƙarsu

An kwashe fiye da kwana bakwai ana fafata yaki tsakanin Iran da Isra’ila, lamarin da ya samo asali daga harin da Isra’ila ta kai wanda Iran ta mayar da martani..

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - A yanzu haka an kwashe fiye da kwana bakwai ana gwabza yaki tsakanin Iran da Isra'ila.

Wannan fada ya yi tsami ne bayan harin da Isra'ila ta kai kan Iran wanda ya yi mutuwar wasu kwamandojinta.

Kasashe da ke goyon bayan Iran ko Isra'ila
Kasashen da ke tare da Iran da waɗanda ke goyon bayan Isra'ila. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Ƙasashe sun rarrabu kan fadan Iran, Isra'ila

Bayan harin Isra'ila, Iran ta mayar da martani a matsayin harin ramuwar gayya wanda ita ma ta yi wa Isra'ila barna mai yawa, cewar rahoton CNN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun daga wannan lokaci ake ci gaba da kai hare-hare a tsakani har zuwa wannan kusan kwana takwas.

Duk da wannan yaki da ake yi, babu kasar da ta shiga domin taimakawa wata a tsakaninsu, amma akwai kasashe da suka fito fili suka nuna wanda suke goyon baya ƙarara a fadan.

Legit Hausa ta duba wasu ƙasashe da ake hasashe ko kuma wadanda suka fito fili domin nuna layinsu.

Kasashen da ke goyon bayan Isra'ila

Yawanci kasashen sun bambanta da irin na'in goyon baya da suke nunawa daya daga cikin masu rikicin.

Wasu alakarsu ba ta wuce ta fannin tattalin arzikida diflomasiyya ba yayin da wasu ke mara musu baya game da rikicin da ake yi.

1. Kasar Amurka

A bayyane yake cewa Amurka na goyon bayan Isra'ila shekaru da dama da suka wuce tun kafin fara wannan fada.

Wasu rahotanni suka ce a yanzu haka Amurka na taimakon Isra'ila a yakin da take yi da Iran.

An ce kasar na kokarin kakkabe jirage marasa matuka da makamai masu linzami a sararin samaniya saboda kare Isra'ila.

Shugaba Donald Trump ya gargadi Iran kan cigaba da fadan inda ya ce nan da mako biyu zai yanke shawarar shiga yakin ko a'a.

Kasar Amurka na nuna goyon baya ga Isra'ila
Kasar Amurka na daga cikin masu goyon bayan Isra'ila. Hoto: Donald Trump.
Asali: Getty Images

2. Kasar Faransa

Kasar Faransa na daga cikin kasashe da rahotanni suka ce suke goyon bayan Isra'ila tun kafin wannan yaki.

Sai dai majiyoyi sun ce ƙasar ba ta fito fili ta nunu goyon bayanta ba amma kasancewarta a cikin kungiyar G7 ya tabbatar da haka.

3. Kasar Burtaniya

Hakanan an bayyana kasar Burtaniya daga cikin ƙasashe da ke goyon bayan Isra'ila a yanzu haka.

Sai dai kaman Faransa suma ba su bayyana ƙarara suna tare da Isra'ila a wannan yaƙi da ake yi ba.

An ce kungiyar ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziki ta G7 suna tare da Isra'ila a wannan yaki da ake yi.

Kasashen sun hada da Amurka, Faransa, Canada, Italy, Burtaniya, Japan da kuma Jamus, cewar rahoton Reuters.

Kasashen da ke goyon bayan Iran

Mafi yawan kasashen da ke goyon bayan Iran Larabawa ne sai kuma wasu daidaiku kamar Rasha da Koriya ta Arewa.

1. Kasar Rasha

Kasar Rasha ta dade a matsayin abokiyar Iran tun kafin ɓarkewar wannan yaki da ake yi, cewar rahoton Al Jazeera.

Rasha na daga cikin kasashen da ke taimakon Iran wurin tabbatar da ta mallaki makamin nukiliya.

Ana hasashen cewa Rasha ta shirya shiga yakin da zarar Amurka ta tsunduma bayan barazana da kasar ke yi wa Iran.

Rasha ta yi gargadi kan yakin Iran da Isra'ila
Rasha na goyon bayan Iran a yakinta da Isra'ila. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

2. Kasar Turkiyya

Majalisar kasar Turkiyya ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai kan Iran a makon da ya wuce inda ta ce hakan barazana ne ga zaman lafiyan duniya.

A cikin wani rubutu a shafin X, gwamnatin ta ce majalisar ta bayyana cewa Isra’ila na amfani da dabarun tada rikici a yankin, inda take kitsa harin Iran da Gaza a lokaci guda.

Hakan ya tabbatar da goyon bayan Turkiyya ga kasar Iran a yakin da ake cigaba da yi a halin yanzu.

3. Koriya ta Arewa

Kasar da ke yankin Asia ta bayyana rashin jin dadi game da harin Isra'ila kan Iran inda ta yi Allah wadai da farmakin.

Wannan ke tabbatar da cewa tana tare da Iran kuma a kowane lokaci za ta iya shiga fadan inda ta gargadi Amurka da Isra'ila.

4. Kasar Pakistan

A wajen taswirar ƙasa, addini da siyasa, akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin Pakistan da Iran.

Islamabad ta sha yin Allah-wadai da hare-haren Isra'ila kan yankin Iran, kamar yadda Fira Ministan kasar, Shehbaz Sharif ya wallafa a shafin X.

A baya-bayan nan, Iran ta ce idan Isra'ila ta ci gaba da cutar da su, to Pakistan za ta kai hari kan Isra'ila da makaman nukiliya.

Duk da cewa Pakistan ta sake jaddada goyon bayanta ga zaman lafiya da diflomasiyya da Iran, Islamabad ta ƙaryata ikirarin da Iran ta yi na cewa Pakistan za ta mayar da martani idan an kai musu hari.

5. Kasar Syria

Sai dai a Siriya, gwamnatin Bashar al-Assad ta rushe kasa da makonni biyu bayan ƙarshen yaƙin Isra’ila da Hezbollah.

Gwamnatinsa ta dade tana zama babban abokiyar Iran a yankin, tana ba ta damar shiga Tekun Rum da kuma zama hanyar isar da kayan tallafi ga Hezbollah.

Sabuwar gwamnati a birnin Dimashƙu na ci gaba da kasancewa cikin rashin jituwa da Tehran, lamarin da ya katse wani muhimmin haɗin kai tsakaninta da Iran a yankin.

6. Kasashen Larabawa

A wani mataki da suka dauka, kasashen Larabawa 20 sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka yi Allah-wadai da harin da Isra'ila ta kai wa Iran.

Sanarwar ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke kara tsananta, wanda ke barazana ga zaman lafiyar yankin tare da goyon bayan Iran.

Majiyoyi suka ce kiran ya fito ne daga kasashen Saudiyya, Masar, Jordan, UAE, Bahrain, Brunei, Turkiyya, Chadi, Aljeriya da sauransu.

Ukraine ta koka kan fadan Iran da Isra'ila

A wani labarin, kasar Ukraine ta nuna damuwa kan cigaba da yaki da ake yi tsakanin kasashen Iran da Isra'ila.

Kiev ta ce wannan yaki ba karamin illata ta zai yi ba duba da mamayar da Rasha ke yi mata.

Kasar ta bayyana goyon bayanta ga kasar Isra'ila duba da kawancen Iran da Rasha wacce abokiyar gabanta ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.