Kasashen Turai na Fafutukar Cimma Tsagaita Wuta yayin da Iran Ta Jefa Makamai Isra'ila

Kasashen Turai na Fafutukar Cimma Tsagaita Wuta yayin da Iran Ta Jefa Makamai Isra'ila

  • Iran ta kaddamar da hari da makamai masu linzami a kudancin kasar Isra’ila yayin da yakin da ake gwabzawa ya shiga rana ta takwas
  • Ministocin harkokin waje daga Iran, Faransa, Jamus da Birtaniya na shirin gana wa don tattauna batun nukiliya da kawo ƙarshen rikicin
  • Hukumomi sun tabbatar da mutane biyar suka jikkata a harin, ciki har da yankin da ke kusa da asibiti da ofishin Microsoft yayin da ake shirin zama

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran – Rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ya ƙara ƙamari a yau, bayan da Iran ta kaddamar da harin makamai masu linzami a kudancin Isra’ila.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ke shirin ganawa da takwarorinsa daga ƙasashen Faransa, Jamus da Birtaniya a birnin Geneva na ƙasar Switzerland.

Ana son kawo karshen yakin Iran da Isra'ila
Kasashen Turai sun fara kokarin shawo kan yakin Isra'ila da Iran Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Aljazeera ta ruwaito cewa ganawar na da nufin tattauna batun shirye-shiryen nukiliyar Iran da kuma matakan kawo ƙarshen hare-haren da Isra’ila ke kai wa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana son kawo karshen yakin Iran da Isra'ila

BBC Hausa ta ruwaito cewa tattaunawar da za a yi a Geneva na iya zama wata dama ta warware rikicin, duba da cewa Iran ta nuna shirin shiga tattaunawa.

Duk da haka, Iran ta ci gaba da harba makamai cikin Isra’ila, ganin cewa sojojin IDF ma ba su daina kai farmaki sassa daban-daban da ke kasar ta ba.

Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda gobara ke ƙone motoci a kusa da ofishin kamfanin Microsoft da ke Beersheba, bayan harin da Iran ta kai a safiyar yau.

Isra’ila: Mutane sun jikkata a harin Iran

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu makamai sun faɗa a yankin asibitin Soroka, kusa da cibiyar fasahar zamani ta Gav-Yam, inda aka bayyana cewa cibiyar ce Iran ta nufi kai wa hari.

Iran ta harba makamai Isra'ila
Iran ta ce ba za ta sassauta wa Isra'ila ba Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Hukumar kashe gobara da ma’aikatan lafiya sun gaggauta kai dauki zuwa wurin da harin ya shafa domin bayar da agaji ga wadanda suka samu raunuka.

Hukumomin kasar Isra'ila sun tabbatar da cewa mutane biyar sun jikkata, amma ba fitar da rahoton rasa rai ba har yanzu.

Iran za ta ci gaba da yakar Isra'ila

A wani labarin, mun wallafa cewa jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi sababbin kalamai da ke ƙarfafa al’ummar ƙasarsa wajen ci gaba da jajircewa a yaki da Isra’ila.

Wannan ya biyo bayan tsanantar rikici tsakanin ƙasashen biyu da ke haddasa fargaba a fadin Gabas ta Tsakiya, wanda ake ganin cewa Amurka ta nuna alamun za ta shiga yakin.

A sakon da ya fitar, Shugaba Khamenei ya bayyana cewa lokaci ya yi da Iran za ta ci gaba da nuna ƙarfi da ƙwazo wajen fuskantar duk wani barazana daga Isra’ila da abokan gabanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.