Kasar Koriya Ta Arewa Ta Goyi bayan Iran, Kim Jong Um Ya Gargadi Isra'ila da Amurka
- Koriya ta Arewa ta caccaki Isra’ila bisa kai farmaki a Iran, tana kiran hakan “laifi ga bil’adama” kuma barazana ga zaman lafiya
- Ta bayyana cewa hare-haren sun lalata cibiyoyin makamashi tare da zargin Isra’ila da ta’addanci kan fararen hula a Iran
- Koriya ta Arewa ta gargaɗi Amurka da Turai su dakatar da shiga lamarin, tana cewa suna hura wutar rikici a Gabas ta Tsakiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Korea - Koriya ta Arewa ta fito karara tana goyon bayan Iran a rikicin da ke kara ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya.
Legit ta rahoto cewa Koriya ta soki Isra’ila bisa farmakin da ta kai a wasu cibiyoyin fararen hula da makamashi na Iran.

Asali: Getty Images
Rahoton TRT World ya nuna cewa Koriya ta fadi haka ne a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na gwamantin kasa ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ya bayyana cewar Isra’ila na aikata “laifin da ba za a yafe mata ba” ta hanyar kashe fararen hula.
Rahoton ya bayyana cewa wannan hali na Isra’ila barazana ce ga zaman lafiya, kuma ana kallon wannan danyen aiki a matsayin shirin tayar da gaba ɗaya yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Kasar Koriya ta Arewa ta gargadi Isra'ila
A cewar sanarwar, Koriya ta Arewa ta bayyana cewa Isra’ila na samun goyon bayan Amurka da kasashen Yammacin duniya, lamarin da ke kara haddasa rikicin da ke faruwa a halin yanzu.
CNA ta rahoto cewa sanarwar ta kara da cewa:
“Isra’ila, wacce Amurka da kasashen Yamma ke karewa, cuta ce ga zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, kuma ita ce babbar barazana ga tsaron duniya baki ɗaya.”
Haka kuma, Koriya ta Arewa ta bayyana damuwarta kan yadda wasu ƙasashen duniya ke kokarin tozarta Iran, saboda tana kare kanta bisa haƙƙinta na ƙasa mai cikakken ‘yanci.
Koriya ta Arewa ta soki Amurka da abokanta
Koriya ta Arewa ta yi kira ga Amurka da kasashen Turai da su dakatar da tsoma baki a rikicin, tana bayyana cewa matakan da suke dauka na kara tabarbarewar lamarin ne.

Asali: AFP
A cewar Koriya ta Arewa:
“Halin da duniya ke ciki yanzu, na nuna yadda rikicin ke kara fitowa fili saboda yadda Amurka da kawayenta ke hura wuta, suna goyon bayan harin da Isra’ila ke kai wa Iran.”
Rahotanni sun nuna cewa wannan matsayi na Koriya ta Arewa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fargabar rikici ya rikide zuwa yaki tsakanin kasashen yankin da duniya baki ɗaya.
Kasashen duniya sun goyi bayan Iran
A wani rahoton, kun ji cewa kasashen duniya sama da 20 ne suka nuna goyon baya ga Iran yayin da take fafatawa da Isra'ila.
Rahotanni sun nuna cewa kasar Saudiyya na cikin kasashen da suka fara nuna goyon baya ga Iran tare da Allah wadai da harin Isra'ila.
Ofishin harkokin wajen Najeriya ya yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai Iran tare da kira a tsagaita wuta a Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng