Ukraine Ta Faɗi Matsalar da Za Ta Faɗa kan Rikicin Isra'ila da Iran, Ta Kama Layinta
- Ukraine na tsoron cewa rikicin Iran da Isra’ila zai dauke hankalin duniya daga yaki da Rasha, kuma hakan zai karfafa Moscow
- Kyiv na goyon bayan harin Isra’ila a Iran, wanda ya rage karfin Tehran wajen tallafa wa Rasha da makamai da kuma goyon bayan soja
- Duk da haka, Volodymyr Zelensky wanda ya hau mulki a 2019 ya nuna damuwa kan yiwuwar rage taimakon Amurka ga Ukraine
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kiev, Ukrain - Rikici tsakanin Iran da kasar Isra’ila na iya karkatar da hankalin duniya daga mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.
Rahotanni sun ce hakan na iya karfafa yunkurin yakin Kremlin, a cewar jami’an Ukraine.

Asali: Getty Images
Damuwar Ukraine kan yakin Isra'ila - Iran
Rahoton da Mechanical Engineering World ya wallafa a Facebook ya ce Kyiv na maraba da harin Isra’ila a kan kasar da ta taimakawa Rasha kai tsaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan rikici ya sa farashin mai ya tashi wanda shi ne babbar hanyar samun kudin shiga da Rasha ke amfani da su wajen daukar nauyin yakin.
“Kalubalen Ukraine shi ne farashin mai, domin idan ya ci gaba da tsada, Rasha za ta ci gaba da samun kudi."
- Cewar wani babban dan siyasar Ukraine
Wannan rikici ya hallaka manyan jami’an sojojin Iran, kuma ya rage karfin rundunar Tehran da hakan na iya hana ta cigaba da tallafa wa Rasha.
Majiyar ta ce:
“Gwamnatin Iran abokiyar Rasha ce, don haka duk abin da suka rasa, alheri ne gare mu, gaba daya, Isra’ila na yi wa duniya gaba daya alheri. Wannan gaskiya ce."

Asali: Getty Images
Hadarin yakin Iran - Isra'ila ga Ukraine
Gwamnatin Shugaba Donald Trump, abokiyar Isra’ila mafi kusa, ta bayyana cewa fifikon tsaronta shi ne Gabas ta Tsakiya da Asiya, ba Turai ba, cewar Punch.
Wannan na iya nufin cewa Rasha za ta ci gaba da samun nasara ko kai hare-haren sama ba tare da martani mai karfi daga Fadar White House ba.
Kokarin Kyiv na neman karin tallafi daga Amurka na fuskantar kalubale saboda dangantakar da ke tsakanin Trump da Shugaban kasar Ukraine, Zelensky.
Zelensky ya tabbatar wa 'yan jarida cewa yaki tsakanin Iran da Isra’ila na da hadari ga Ukraine.
Ya ce:
“Babu wanda ke ikirarin cewa dangantakarsa ta fi ta Amurka da Isra’ila muhimmanci, amma muna son a ci gaba da tallafawa Ukraine."
Ya yi nuni da yakin Isra’ila da Hamas a Gaza bayan harin da aka kai ranar 7 ga Oktoba, 2023 a matsayin misali.
Jami’ai a ofishin Zelensky sun ce bayan barkewar rikicin Gaza cewa hakan ya sa Ukraine ta mai da hankali wajen bunkasa masana’antun makamanta.
Rasha ta jefa dubban jirage marasa matuƙi da makamai masu linzami kan Ukraine tun bayan fara mamayarta a shekarar 2022, ciki har da makamai da Iran ta kera ko ta tsara.
Iran ta yi wa kasar Isra'ila barna
Kun ji cewa Iran ta kai wa wani asibiti a Beersheba a Israila hari bayan makami mai linzami da ta harba a kasar.
Lamarin da ya jikkata mutane da dama yayin da Ministan tsaron Isra’ila ya ce “ba za a bar Ayatullah Ali Khamenei ya ci gaba da rayuwa ba,” saboda hare-hare.
Sojojin Isra’ila a bangarensu sun kai farmaki kan sansanonin nukiliyar Iran da suka hada da Arak da Natanz.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng