Adadin Musulman Duniya da Suka Halarci Aikin Hajjin 2026 Ya Haura Miliyan 1.7

Adadin Musulman Duniya da Suka Halarci Aikin Hajjin 2026 Ya Haura Miliyan 1.7

  • Hukumar ƙididdiga ta Saudiyya ta sanar da cewa mahajjata miliyan 1.7 ne suka gudanar da aikin Hajjin 2026, adadin da ya zarce na 2025
  • Mahajjata daga sassa daban-daban na duniya sun gudanar da ibadu a Arafah, Muzdalifah da Mina cikin tsauraran matakan tsaro
  • Wasu mahajjata sun bayyana aikin Hajjin a matsayin aikin da ake yi cikin tsananin zafi, amma mai cike da shauki na samun kusanci da Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Saudiyya - Hukumar Kididdiga ta Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa jimillar alhazan da suka gudanar da aikin Hajjin 2026 ta kai mutum 1,707,301.

Alƙaluman da aka fitar bayan kammala aikin Hajjin shekarar 1447AH sun nuna ƙarin alhazai idan aka kwatanta da bara da aka samu mutum 1,673,230.

Saudiyya ta bayyana cewa fiye da mahallata miliyan 1.7 suka yi aikin Hajjin 2026.
Miliyoyin Musulmai suna gudanar da Sallah a masallacin Ka'abah, yayin aikin Hajjin 2026. Hoto: Zain JAAFAR / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Musulmai miliyan 1.5 sun shiga Saudiyya

Kara karanta wannan

2026: Muhimman abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

Hukumar ta bayyana cewa kididdigar ta ƙunshi dukkan maza da mata da suka halarci aikin Hajjin bana a birnin Makkah da sauran wurare masu tsarki, in ji rahoton Aljazeera.

Kwamandan rundunar fasfo ta Hajji, Saleh bin Saad al-Murabba, ya ce sama da alhazai miliyan 1.5 sun shiga ƙasar zuwa ranar Juma’a, yayin da ake sa ran ƙarin zuwan wasu.

Musulmi daga sassa daban-daban na duniya sun hallara a Saudiyya domin gudanar da ibadu da ayyukan Hajji a Arafah, Muzdalifah da Mina.

Mahukuntan Saudiyya sun kuma tura jami’an tsaro, ma’aikatan lafiya da kayan aiki domin tabbatar da tsaro da jin daɗin alhazai yayin gudanar da ibadar.

Muhimmancin aikin Hajji ga Musulmi

Aikin Hajji na ɗaya daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar kuma wajibi ne ga duk musulmin da yake da hali da lafiya ya yi shi sau ɗaya a rayuwarsa.

Ga mutane da dama, isa birnin Makkah cikar babban buri ne da suka daɗe suna fata, kamar yadda rahoton Gulf News ya nuna.

Wata hajiya daga Masar mai suna Samya Abdul Moneim ta bayyana farin cikinta bayan samun damar gudanar da aikin Hajjin bana.

Kara karanta wannan

Goron Sallah: Gwamnan Kano ya gwangwaje ma'aikatan jiharsa da kyautar kudi

Ta ce:

“Ina cikin ni’ima da farin ciki. Wannan wani yanayi ne da nake ji da ba zan iya bayyana shi ba. Alhamdulillah, ina cikin wata babbar ni’ima.”
Musulmai sun bayyana cewa aikin Hajji na daga cikin aikin da ke kusanta baya ga Allah.
Dandazon Musulmi suna gudanar da aikin Hajji a 2026. Hoto: Zain JAAFAR / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Alhazai sun jure zafin rana

Kafin tafiya zuwa Mina, alhazai sun kasance suna dawafi a kusa da Ka’aba cikin tsananin zafin rana, inda wasu ke amfani da lema da fan domin rage zafi, in ji rahoton Daily Trust.

Masu aikin sa kai sun rika rabon ruwa da kayan sanyaya iska domin taimaka wa alhazai.

Wani masanin kimiyyar siyasa daga Amurka, Youssef Chouhoud, ya ce aikin Hajji ya sauya masa tunani da rayuwa baki ɗaya.

Ya ce:

“A gare ni, wannan Hajji tamkar sabon babi ne a rayuwata. Duk da tsananin zafi da wahala, yin aikin Hajji na sanya wani shauki na kusanci ga Allah da ba zai misaltu ba.”

Fassarar hudubar Arfa a harsuna 45

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Saudiyya ta sanar da cewa za a fassara hudubar Arfa ta bana zuwa harsuna 35 ciki har da Hausa da Yarbanci.

Kara karanta wannan

Hajji 2026: Za a fassara huɗubar Arfa zuwa Hausa da wasu harsuna 34 na duniya

An ce za a yada hudubar ta kafafen kafofin sadarwa na zamani domin miliyoyin alhazai da Musulmai su saurara da yarensu.

Saudiyya ta kuma gargadi ƙasashen da ke halartar aikin Hajji su bi dokoki domin tabbatar da tsaro da nasarar aikin bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com