"Za Su Dandana Kudarsu," Iran Ta Yi Watsi da Barazanar Kasar Amurka

"Za Su Dandana Kudarsu," Iran Ta Yi Watsi da Barazanar Kasar Amurka

  • Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gargaɗi ƙasar Amurka da kada ta shiga yaƙin da ta ke da Isra’ila matuƙar ba jan kunne da ta yiwa kawarta ba
  • Wannan ya biyo bayan kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump da ke nuna cewa akwai yiwuwar kasarsa ta kai mummunan hari a Iran
  • Wasu rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka gwamnatin Amurka na shiri, dakarunta za su iya kaddamar wa Iran hari a karshen mako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar IranJagoran kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi watsi da kiraye-kirayen Amurka na neman Iran ta mika wuya yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai mata hare-hare.

A yau Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025 ne aka shiga kwana na shida ana musayar manyan makamai a tsakanin kasashen Iran da Isra'ila.

Shugaban Amurka, Donald J Trump
Iran ta gargadi Amurka Hoto: Getty
Asali: Getty Images

AP News ta ruwaito cewa wannan shi ne karo na biyu da Khamenei ya bayyana a bainar jama'a tun bayan da hare-haren suka fara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuma hakan ya zo ne kwana guda bayan da Amurka ta sake sabunta barazanar ta.

Iran ta yi watsi da barazanar Amurka

BBC Hausa ta ruwaito Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya tura sako kai tsaye ga Amurka.

Ya ja kunnen mahukuntan da ke Washington game da yiwuwar tsoma baki a rikicin da ke ci gaba tsakanin Iran da Isra’ila.

Gharibabadi, yayin wani jawabi da kafafen yada labaran gwamnati suka ruwaito, ya ce Iran ba za ta zura ido tana kallo ba idan har Amurka ta mara wa Isara'ila baya ba.

Shugaban Amurka ya yiwa Iran barazana
Iran ta yi watsi da barazanar Amurka Hoto: Donald J Trump
Asali: Twitter

Ya ce:

"Idan Amurka ta tsunduma kai tsaye cikin rikicin da niyyar taimakon Isra’ila, to tabbas za mu koya darasi da ba za su manta da shi ba. Za mu tsaya tsayin daka wajen kare martabar ƙasarmu.”

Iran ta gargadi kasar Amurka

Gharibabadi ya ci gaba da cewa Iran ba za ta zauna jiran kiran sulhu ba idan aka ci gaba da kai mata hari, yana mai cewa:

“Muna ba Amurka shawara da ta yi nisa da rikicin, ko kuma ta tilasta wa Isra’ila dakatar da harin da take kai mana. Idan hakan ya gagara, muna da dukkanin matakan kariya da suka dace da kare kanmu daga kowanne irin barazana.”

Iran ta dade tana zargin Amurka da marawa Isra’ila baya a ayyukanta na farmaki, musamman a lokacin da yanayin yaki ke kara tsananta a Gabas ta Tsakiya.

Amurka na shirin kai hari a Iran

A baya, mun wallafa cewa Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa, gwamnatin Amurka na shirin kai hari kan Iran cikin 'yan kwanakin nan, musamman a karshen mako.

Wannan lamari na zuwa ne yayin da tashin hankali tsakanin Iran da Isra’ila ke karuwa, sa'ilin da aka shiga kwana na shida ana musayar miyagun makamai da kashe jama'a.

A ranar Laraba, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a gaban manema labarai a fadar White House cewa ta yiwu ya shigar wa Isra'ila yaƙin, babu wanda ya san aniyarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.