Ana Wata ga Wata: Shugaba Kim Jong Un Ya Harba Manyan Makamai

Ana Wata ga Wata: Shugaba Kim Jong Un Ya Harba Manyan Makamai

  • Koriya ta Arewa ta harba wani abu da ba a tantance ba a gabar tekunta ta yamma a ranar Talata, kamar yadda rundunar sojin Koriya ta Kudu ta fada
  • Harin ya biyo bayan wani harin da Koriya ta Arewa ta kai a watan da ya gabata, inda ta harba makamai masu linzami masu gajeren zango da dama
  • Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya mayar da hankali wajen fadada makaman nukiliya tare da nuna rashin jituwa da gwamnatin Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

North Korea - Koriya ta Arewa ta harba wani abu da ba a tantance ba daga gabar tekunta a ranar Talata, kamar yadda rundunar sojin Koriya ta Kudu ta bayyana, a wani abu da ake ganin shi ne sabon gwajin makamai na kasar a bana.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Tinubu ya cancanci 'yan Najeriya su kara ba shi dama a zaben 2027

Takaitaccen bayani daga babban hafsan sojin Koriya ta Kudu bai bayar cikakken bayani ba game da hakikanin abin da ya faru bayan harba makaman.

Shugaba Kim Jong Un
Kim Jong Un a hagu, wani jirgin ruwa da aka kai wa hari a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Makaman da aka harba a baya

AP ta wallafa cewa lamarin ya biyo bayan wani harin da Koriya ta Arewa ta kai a ranar 19 ga Afrilun 2026, inda ta harba makamai masu linzami da dama.

Kafafen yada labaran gwamnatin Koriya ta Arewa sun bayyana harba makaman a matsayin nuna karfin kananan bama-bamai masu tarwatsewa.

Koriya ta harba makamai teku

An bayyana harba makaman da Koriya ta Arewa ta yi a ranar Talata a matsayin cigaba da nuna karfin soja da neman jefa fargaba ga wadanda suke takun saka da su.

Harin ya zo ne sa’o’i bayan shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae Myung ya bukaci a kara kokari wajen bunkasa rundunar sojin kasar a yayin taron majalisar ministoci.

Ya jaddada muhimmancin fasahar zamani da jiragen yaki marasa matuka da kuma yiwuwar mallakar jirgin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya, wani batu da ya kasance cikin tattaunawarsa da Amurka.

Kara karanta wannan

'Babu afuwa': Babban limami ya fadi abin da Kur'ani ya ce kan yan ta'adda

Washington Post ta ce Lee bai yi tsokaci kai tsaye kan barazanar da Koriya ta Arewa ke haifarwa ba, amma ya jaddada muhimmancin Koriya ta Kudu ta nuna shirin kare kasarta da kanta.

Kim Jong Un
Kim Jong Un bayan harba makami a teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Koriya na fadada shirin nukiliya

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya ci gaba da fadada makaman nukiliya da na makamai masu linzami tun bayan rushewar tattaunawar nukiliya tsakaninsa da shugaban Amurka, Donald Trump a shekarar 2019.

Trump ya sha bayyana aniyarsa ta dawo da tattaunawa da Kim, amma Pyongyang ta yi biris da bukatun tare da neman Amurka ta daina neman Koriya ta Arewa ta watsar da makaman nukiliyarta a matsayin sharadin tattaunawa.

Kim ya dauki matsaya mai tsauri kan Koriya ta Kudu, wacce ya ayyana a matsayin makiya mafi muni kuma ta dindindin ga kasarsa.

Amurka ta kai hari Iran

A wani labarin, mun kawo muku cewa Amurka ta kai sababbin hare-haren sama kan Iran, tana mai cewa an kai harin ne domin kare kai.

Kyaftin Tim Hawkins na rundunar ya ce dakarun Amurka sun kai hare-haren kare kai a Kudancin Iran domin kare sojojin su daga barazanar dakarun Iran.

Kakakin rundunar ya kara da cewa abubuwan da aka kai wa hari sun hada da wuraren harba makamai masu linzami da kuma jiragen ruwan Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng