Rasha Ta Goyi bayan Iran, Putin Ya Gargadi Trump kan Taya Isra'ila Fada

Rasha Ta Goyi bayan Iran, Putin Ya Gargadi Trump kan Taya Isra'ila Fada

  • Shugabannin Rasha da China sun caccaki hare-haren Isra’ila a kan Iran, suna masu kira da a bi hanyar diflomasiyya wajen warware rikicin
  • Moscow ta fitar da gargadi mai ƙarfi ga Amurka da kada ta tsoma baki a rikicin, tana cewa hakan zai janyo mummunan rikici a fadin duniya
  • Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya nemi zama mai sasantawa tsakanin Isra’ila da Iran, bayan tattaunawa da Netanyahu da shugaban Iran

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Rasha da China sun hada kai wajen bayyana matsayinsu kan rikicin da ke kara tsananta tsakanin Isra’ila da Iran.

Kasashen biyu sun caccaki matakin Isra’ila na kai hari kan Iran tare da yin kira da a dakatar da tashin hankali.

Rasha ta yi adawa da kokarin Trump na shiga yakin Iran da Isra'ila
Rasha ta yi adawa da kokarin Trump na shiga yakin Iran da Isra'ila. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton France 24 ya nuna cewa shgabannin kasashen biyu sun tattauna ta wayar tarho kan rikicin Iran da Isra'ila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne yayin da shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yana tunanin ko zai shiga yakin domin taya Isra’ila ko a’a.

Rasha ta gargadi Amurka kan shiga yakin

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova, ta gargadi Amurka da kada ta kuskura ta tsoma baki a rikicin tsakanin Isra’ila da Iran.

BBC ta rahoto cewa Maria Zakharova ta ce:

“Muna fatan fadakar da Washington cewa duk wani matakin soja daga gareta zai zama mataki mai hatsari kuma zai haifar da mummunan sakamakon da ba a tsammani.”

Sanarwar ta kara da cewa dole ne a kauce wa tsoma baki da zai iya jefa yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya cikin wani sabon rikici mai tsanani.

Xi Jinping: 'Daina fada ya fi komai muhimmanci'

A cewar rahotannin da Legit Hausa ta tattaro, Xi Jinping ya shaida wa Putin cewa dakatar da rikici shi ne abu mafi muhimmanci a halin yanzu.

Ya ce:

“Karfin soji ba shi ne mafita ga rikicin duniya ba. Dole ne a dakatar da tashin hankali da wuri, musamman daga bangaren Isra’ila, domin hana rikicin ya wuce kima.”

Xi ya jaddada cewa akwai bukatar kowane bangare, musamman Isra’ila, ya dakatar da hare-hare domin a samu a shawo kan rikicin da ke ci gaba da fadada.

Putin na neman yin sulhu tsakanin Isra'ila da Iran
Putin na neman yin sulhu tsakanin Isra'ila da Iran. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Iran da Isra'ila: Putin ya nemi zama mai sulhu

Shugaban Rasha Vladimir Putin na kokarin taka rawa a matsayin mai sulhu tsakanin Isra’ila da Iran, inda ya yi kira da a koma teburin sulhu.

Putin ya riga ya yi tattaunawa da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, inda ya nuna aniyar sa ta shiga tsakani domin sasanta bangarorin biyu.

Isra'ila ta ce za ta cigaba da kai hari Iran

A wani rahoton, kun ji cewa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce Iran za ta dandana kudarta kan wani hari da ta kai musu.

Rahotanni sun nuna cewa Netanyahu ya yi magana ne bayan wani hari da Iran ta kai musu da sassafe.

Ministan tsaron Isra'ila ya bukaci dakarun kasar da su kara kaimi da shiri domin cigaba da zafafa kai hare hare kasar Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng