'Bola Tinubu Zai Samu Kuri'u Sama da Miliyan 10 a Zaben Shugaban Kasa na 2027'

'Bola Tinubu Zai Samu Kuri'u Sama da Miliyan 10 a Zaben Shugaban Kasa na 2027'

  • Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi ikirarin cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu kuri'u fiye da miliyan 10 a babban zabe
  • Yilwatda ya bayyana adadin dalibai da talakawan da za su zabi Bola Tinubu saboda suna amfana da shirye-shiryen gwamnatinsu ta APC
  • Ya kuma musanta rade-radin cewa APC ke haddasa rigingimu a jam'iyyun adawa da nufin nakasa su kafin babban zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa jam’iyya mai mulki za ta samu sama da ƙuri’u miliyan 10 a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Wannan kalamai na shugaban APC na zuwa ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben fitar da gwanin jam’iyyar, inda ya samun ƙuri’u miliyan 10.9.

Kara karanta wannan

NDC ta yi zargin wasu shugabanninta na karbar na goro domin tsayar da 'dan takara

Shugaban APC.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda a yana jagorantar taron kwamitin gudanarwa (NWC) a Abuja Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Farfesa Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Politics Today na Channels tv a ranar Litinin.

Yadda Bola Tinubu zai samu kuri'u a 2027

Da aka tambaye shi ko APC za ta iya maimaita irin wannan adadi a babban zaɓen ƙasa, Yilwatda ya ce tushen magoya bayan jam’iyyar ya zarce yawan waɗanda suka yi rajista a cikinta.

“Fiye da haka ma, waɗannan duk mambobinmu ne,” in ji shi.

Farfesa Yilwatda ya yi magana kan masu cin gajiyar shirye-shiryen gwamnati, yana mai cewa miliyoyin ‘yan Najeriya da ke amfana da gwamnatin tarayya za su iya zama ƙuri’un APC a 2027.

“A tunanina, yawancin ɗalibai mambobin jam’iyyarmu ne. Muna da kusan ɗalibai miliyan 1.5 da ke cin gajiyar shirin rancen karatu.
"Gwamnati ta biya masu kuɗin makaranta gaba ɗaya, kuma da yawa daga cikinsu suna da iyaye, ‘yan’uwa da iyalai,” in ji shi.

Jam'iyyar APC ta tuna fa tsarin inshora

Kara karanta wannan

2027: Mohammed Abacha ya sha kaye, PDP ta tsaida dan takarar gwamna a jihar Kano

Shugaban APC ya ƙara da cewa masu cin gajiyar tsarin inshorar lafiya na ƙasa da kuma ma’aikatan da ke aiki a manyan ayyukan ƙasa su ma za su iya mara wa jam’iyyar baya.

“Mun ƙara sama da ‘yan Najeriya miliyan huɗu cikin tsarin inshorar lafiya, musamman tsofaffi da marasa ƙarfi. Kana ganin za su zaɓi wata jam’iyya daban bayan tamu?” ya tambaya.

Yilwatda ya kuma ambaci ayyuka kamar titin Lagos-Calabar, aikin titin Badagry da layin dogo da ke haɗa Kano, yana mai cewa dubban ‘yan Najeriya na amfana kai tsaye ko a kaikaice daga waɗannan ayyuka.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yayin kaddamar da wasu ayyuka a jihar Delta Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

APC ta musanta hada yan adawa fada

Ya jaddada cewa APC ita ce jam’iyyar siyasa mafi tsari a Najeriya, yana mai cewa tana da kusan mambobi miliyan 12.7 da suka yi rajista a faɗin ƙasar nan, kamar yadda Vanguard ta rahoto

Haka kuma, ya musanta zargin cewa APC ce ke haddasa rikice-rikice a jam’iyyun adawa, yana mai cewa Shugaba Tinubu ba ya kakaba wata jam’iyyar ‘yan takara.

Dalilin da zai sa a sake zaben Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Ministan lafiya, Muhammad Ali Pate, ya yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci wa'adi na biyu.

Kara karanta wannan

"Kamar nadin sarauta," Masani ya yi kaca kaca a nasarar da Tinubu ya samu a APC

Ministan ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya cancanci yan Najeriya su sake zaɓensa karo na biyu duba da nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

Ya kuma yaba wa gwamnatin Tinubu bisa samar da damar aikin yi ga matasan Najeriya, yana mai cewa matasa sama da 3,000 a Bauchi sun samu aiki

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262