Air India: Maganar Karshe da Wata Mata Ta Yi da Mijinta kafin Ya Mutu a Hatsarin Jirgi
- An bayyana tattaunawar ƙarshe tsakanin wata mata da mijinta, wanda ya rasu a hatsarin jirgin Air India mai lamba AI171 a Ahmedabad
- Jirgin kirar Boeing 787-8 Dreamliner, wanda ke kan hanyar zuwa London, ya faɗi jim kaɗan bayan tashinsa daga Sardar Vallabhbhai Patel
- Abokin mamacin ya bayyana matuƙar alhininsa tare da jajanta wa iyalan Ketan Shah bayan wannan hatsari da ya yin silar mutuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
India - An fito da tattaunawar ƙarshe da aka yi tsakanin wata mata da mijinta, Ketan Shah, wanda ke cikin jirgin Air India da ya yi hatsari.
Jirgin ya yi hatsari ne jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin sama na Sardar Vallabhbhai Patel da ke Ahmedabad, India, a ranar 12 ga Yuni, 2025.

Asali: UGC
Mata ta rasa mijinta a hatsarin Air India
Kamar yadda BBC ta ruwaito, Ketan Shah ya je India ne domin duba mahaifinsa da ke rashin lafiya kuma yana shirin komawa ga iyalinsa a Burtaniya kafin mummunan hatsarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce Ketan Shah, wanda ke da shekaru 43 a duniya, yana da kantin sayar da kayayyaki a ƙauyen Shipton Bellinger da ke kan iyakar Hampshire da Wiltshire.
Jigneshkumar Patel, wanda ya shafe shekaru 15 yana abokantaka da Ketan Shah, ya bayyana yadda labarin ya shafe shi da kuma dalilin da ya sa ya damu da iyalan mamacin.
Maganar karshen Shah kafin hatsarin Air India
Jigneshkumar Patel ya bayyana tattaunawar ƙarshe da Ketan Shah ya yi da matarsa, Megha, kafin hatsarin jirgin ya kawo ƙarshen rayuwar abokin na sa.
"Kafin jirgin ya tashi, ya kira matarsa ya gaya mata yana cikin jirgin kuma wannan ce tattaunawar ƙarshe da ta yi da shi."
- Jigneshkumar Patel.
Patel ya kuma bayyana abin da ya yi lokacin da ya fara jin labarin hatsarin, inda ya ce:
"Da safe mun ji labarin faɗuwar jirgi, kuma muka gane cewa Shah zai yi tafiya a wannan ranar amma ba mu da tabbacin yana cikin jirgin."
Bayan ganin sunan Ketan Shah a jerin fasinjoji, Patel ya ce ya tuntubi matar abokin na sa, wadda ta tabbatar masa cewa mijinta yana cikin jirgin.
Ya ce abokinsa ya zauna a garin Southbourne da ke a Dorset sama da shekaru 10, kuma yana da 'ya'ya biyu: Mace da namiji.

Asali: UGC
Air India: Ramesh ya halarci jana'izar ɗan'uwansa
Vishwash Kumar Ramesh, wanda shi ne kaɗai wanda ya tsira daga hatsarin jirgin Air India, ya halarci jana'izar ɗan'uwansa, Ajay, wanda ya mutu a hatsarin.
Duk da roƙon da 'yan uwansa suka yi masa kada ya halarci jana'izar saboda rashin lafiyarsa, Vishwash Ramesh ya nace kuma yana ɗaya daga cikin masu ɗaukar gawa.
Ya yi kuka yayin da mutane ke yi masa gaisuwa a wajen taron. Mutane da yawa da suka kalli bidiyon bikin sun tausaya masa, kamar yadda BBC India ta wallafa a Instagram.
Abin da ake zargin ya jawo hatsarin Air India
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ana zargin cewa wani mummunan kuskure da ya faru yayin tashin jirgin Air India ne ya haddasa hatsarin da ya kashe mutum 241.
Masanin harkar sufurin jiragen sama, Captain Steve, ya bayyana cewa hadarin na da nasaba da kuskuren matukin jirgin wajen daka tayoyin sauka.
Sai dai, wannan ra’ayi na Captain Steve har yanzu ba tabbaci ba ne, domin hukumomin bincike na ci gaba da nazarin lamarin don gano hakikanin musabbabi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng