Hajji 2026: Za a Fassara Huɗubar Arfa zuwa Hausa da Wasu Harsuna 34 na Duniya
- Mahukuntan Saudiyya sun sanar da cewa za a fassara hudubar Arfa ta bana zuwa harsuna 35 ciki har da Hausa da Yarbanci
- An ce za a yada hudubar ta kafafen kafofin sadarwa na zamani domin miliyoyin alhazai da Musulmai su saurara da yarensu
- Saudiyya ta kuma gargadi ƙasashen da ke halartar aikin Hajji su bi dokoki domin tabbatar da tsaro da nasarar aikin bana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Saudiyya - Mahukuntan Saudiyya sun sanar da cewa za a fassara hudubar Arfa ta bana zuwa harsuna 35 tare da yaɗa ta ta kafafen sadarwa na zamani da wasu tashoshi masu alaƙa da aikin Hajji.
An bayyana cewa matakin zai bai wa miliyoyin alhazai da Musulmai a duniya damar sauraron hudubar cikin yarensu na asali.

Source: Getty Images
Shugabancin harkokin addini na Masallacin Harami da Masallacin Annabi ne ya bayyana hakan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Hausa na cikin harsunan da aka zaɓa
Rahotanni sun nuna cewa harsunan da za a yi amfani da su sun haɗa da manyan harsunan duniya daga Afirka, Asiya da Turai.
Cikin harsunan akwai Turanci, Faransanci, Hausa, Yarbanci, Urdu, Indunusiyanci, Turkish, Persian, Sinanci, Rashanci, Hindi da Swahili.
Sauran harsunan sun haɗa da Somali, Punjabi, Tamil, German, Portuguese, Malay, Bosnian da Lithuanian.
Abdulrahman Sudais ya bayyana manufar fassara hudubar
Shugaban harkokin addini na Saudiyya, Sheikh Abdulrahman Al-Sudais, ya ce an shirya yin fassarar ne domin isar da saƙonnin ubangiji da koyarwar Musulunci ga Musulmai da ba sa jin Larabci.
Ya ce:
“Aikin fassarar hudubar Arfa na daga cikin manyan shirye-shiryen da aka gina bisa shekaru na gogewa domin Musulmai marasa jin Larabci su amfana da saƙonnin hudubar.”
Sudais ya ƙara da cewa an tattara manyan kayan fasaha da ƙwararrun ma’aikata domin tabbatar da hudubar ta isa ga jama’a cikin inganci.
Hudubar Arfa na daga cikin manyan hudubobin Musulunci da ake gabatarwa duk shekara a Dutsen Arafat yayin aikin Hajji.
Miliyoyin Musulmai a duniya kan saurari hudubar saboda muhimmancinta a addinin Musulunci.

Source: Getty Images
Saudiyya ta gargadi ƙasashen da ke aikin Hajji
A wani ɓangare kuma, mahukuntan Saudiyya sun sake jan kunnen ƙasashen da ke halartar aikin Hajji su bi ƙa’idojin aikin domin tabbatar da tsaro da gudanar da Hajji cikin nasara.
Sun ce ƙasashen za su ɗauki alhakin duk wata matsala da ta taso idan ba su wayar da kan alhazansu yadda ya kamata ba, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.
An kuma buƙaci shugabannin tawagogin Hajji su tabbatar alhazai suna tafiya cikin rukuni domin rage ɓacewar mutane a wuraren ibada.
Haka kuma, hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa sashen fasahar sadarwa na hukumar ya fara ƙoƙarin mayar da ayyukan Hajji gaba ɗaya zuwa tsarin fasahohin zamani.
Abin da zai faru ranar Arfar 1447
A wani labari, mun ruwaito cewa, wani abin mamaki dangane da ilimin taurari zai faru a ranar Arfa ta shekarar 2026, inda rana za ta yi daidai a saman Ka’aba a birnin Makka.
Masana sun ce wannan lamari yana faruwa ne sau ɗaya cikin shekara 139 idan ya zo daidai da ranar Arfa, kuma ana sa ran zai faru a bana.
Hukumomin hasashen yanayi na Saudi sun ce lamarin ba yana nufin za a samu matsananciyar zafi ba, tare da yin karin bayani game da halin da za a shiga.
Asali: Legit.ng


