Namadi Sambo Ya Karyata Komawa APC, Ya Fadi Matsayarsa a Siyasar Najeriya
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, ya karyata jita-jitar da ke cewa ya koma jam’iyyar APC mai mulki bayan fita daga PDP
- Sanarwa daga mai magana da yawunsa ta ce hoton da ke yawo tare da Gwamna Uba Sani tsohon hoto ne da aka ɗauka shekaru da suka wuce
- Namadi ya ce halartar taron kaddamar da asibiti ba yana nufin sauya sheƙa ba ne, domin aikin asibitin yana cikin ayyukan da ya samar a baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya fito fili ya karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya sauya sheƙa zuwa APC.
Wannan na zuwa ne bayan wani hoto da ya karade dandalin sada zumunta wanda ke nuna Namadi Sambo tare da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.

Asali: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan karyata rade radin ne a cikin wani sako da tsohon hadiminsa, Umar Sani ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
BBC ta rahoto cewa a sanarwa da tsohon mai taimaka masa a fannin yaɗa labaran ya fitar, an bayyana jita-jitar a matsayin ƙarya da ruɗani da nufin yaudarar al’umma.
Hoton ya janyo ce-ce-ku-ce da ya sa ake zargin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya koma APC.
Namadi Sambo: 'Hoto na da Uba Sani tsoho ne'
Sanarwar ta ce hoton da ya janyo ce-ce-ku-ce da ya nuna Namadi Sambo da Gwamna Uba Sani, hoto ne da aka ɗauka shekaru da suka wuce, lokacin da gwamnan ya kai masa ziyarar jaje.
An bayyana cewa ziyarar ta gudana ne a gidan Namadi da ke Abuja bayan rasuwar ɗan uwansa, marigayi Sani Sambo, kuma ba ta da alaka da wata manufa ta siyasa.
Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce:
“Wasu na ƙoƙarin amfani da hoton domin yaudarar jama'a da ƙirƙirar labarin da ba shi da tushe ne kawai,”
Dalilin haduwar Namadi Sambo da Uba Sani
Sanarwar ta kuma yi karin haske kan halartar da Namadi Sambo zai yi wajen kaddamar da gadaje 300 a Jihar Kaduna a ranar 19 ga Yuni, 2025.
An bayyana cewa wannan taron yana da nasaba da aikin da Namadi ya faro ne tun lokacin da yake ofis a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.
Saboda haka aka bayyana cewa halartarsa wajen ba wani alamu ne na goyon bayan wata jam’iyya ba.
Sanarwar ta ce:
“Babu wani yunƙuri daga Namadi na sauya sheka zuwa kowace jam’iyya,”

Asali: Facebook
Namadi ya jaddada kasancewarsa a PDP
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa har yanzu shi mamba ne na jam’iyyar PDP, kuma babu wani shiri da ya ke da shi na barin jam’iyyar.
Sanarwar ta ce duk wani yunƙuri da ake yi na haɗa shi da wata jam’iyya ta daban wani shiri ne na ɓata suna da ɓata gari a siyasa ke yi.
Namadi Sambo ya hadu da Atiku a Osun
A wani rahoton, kun ji cewa tsofaffin mataimakan shugaban kasa, Namadi Sambo da Atiku Abubakar sun hadu da juna a Osun.
A lokacin da suka hadu a filin jirgin sama, an hango Atiku Abubakar tare da wani mutum da ake tsammanin Yemi Osinbajo ne.
Atiku ya kai ziyara jihar Osun ne yayin da ya ke kan hanyar zuwa jihar Ondo domin shaida bikin sarautar gargajiya da aka gayyace shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng