Kaico: Mahaifi Ya Hallaka 'Yarsa yayin Hatsaniya a Kano

Kaico: Mahaifi Ya Hallaka 'Yarsa yayin Hatsaniya a Kano

  • Wani magidanci ya hallaka ƴarsa yayin wata ƴar hatsaniya da ta auku a tsakaninsu a cikin gida
  • Magidancin ya hallaka ƴar tasa ne sakamakon bugun da ya yi da wani abu mai nauyi a kanta wanda ya yi sanadiyyar rasuwarta
  • Jami'an ƴan sanda sun yi gaggawar zuwa wajen da lamarin ya auku domin fara gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Ana zargin wani mutum mai shekaru 60 da haihuwa, mai suna Adamu Mohammed, da laifin kashe ƴarsa mai shekaru 18, Zainab Adamu.

Ana zargin mutumin da kashe ƴarsa a lokacin wata hatsaniya da ta faru a cikin gida a unguwar Dawakin Dakata da ke cikin birnin Kano.

Magidanci ya kashe 'yarsa a jihar Kano
Wani magidanci ya hallaka 'yarsa a Kano Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda magidanci ya kashe ƴarsa a Kano

Majiyoyi sun bayyana cewa wannan mummunan lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin da misalin ƙarfe 5:00 na Asuba.

Lamarin ya auku ne a lokacin da Adamu Mohammed ya bugi ƴarsa da wani abu mai nauyi a yayin wata hatsaniya da suka yi a gida, wanda hakan ya sa ta suma.

Wani mazaunin unguwar, wanda ya damu da abin da ya gani, ya yi gaggawar kiran jama’a misalin awa biyu bayan faruwar lamarin, abin da ya jawo al’ummar yankin suka gaggauta kawo ɗauki.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa ƴan sanda sun isa wurin da lamarin ya faru cikin sauri domin gudanar da bincike.

An garzaya da Zainab Adamu zuwa asibitin ƙwararru na Sir Sunusi da ke cikin Kano, inda likitoci suka tabbatar da cewa ta riga mu gidan gaskiya.

Bayan an kammala binciken farko da likitoci suka yi, an miƙa gawar marigayiyar ga iyalinta domin a yi mata jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci.

Ƴan sanda na ci gaba da bincike

Majiyoyi daga rundunar ƴan sanda sun tabbatar da kama wanda ake zargi, Adamu Mohammed, inda suka bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin wannan ɗanyen aikin da ya aikata ga ƴarsa.

Magidanci ya halalka 'yarsa har lahira a Kano
'Yan sandan sun cafke magidancin da ya kashe 'yarsa a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wasu daga cikin mazauna unguwar sun bayyana wannan lamari a matsayin abin firgici da girgiza zuciya.

Mutanen sun yi kira ga hukumomi da su ƙara kokari wajen wayar da kan jama’a da kuma ɗaukar matakai na hana ƙaruwar tashin hankali da cin zarafi a cikin gida, musamman tsakanin ƴan uwa na jini.

Sun ce irin wannan mummunan aiki na ƙara yawan tashe-tashen hankula a cikin al’umma, kuma akwai bukatar a dinga shawo kansu kafin su kai ga hallaka rayuka.

Ƴan bindiga sun kai hari a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kebɓi.

Ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen Tadurga da ke cikin ƙaramar hukumar Zuru a cikin dare, inda suka riƙa yin harbi kan mai uwa da wabi.

Tsagerun sun hallaka mutane da dama tare da yin awon gaba da wasu daban waɗanda ba a san adadinsu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng