Aikin Hajji: An Cafke Iyalan 'Dan Bindiga Ado Aliero a Birnin Madina a Saudiyya
- Ana rade radin hukumomin Saudiyya sun cafke wasu mata biyu da ake zargi da kasancewa uwa da matar jagoran ‘yan bindiga, Ado Aliero
- Rahotanni sun ce an kama su ne a birnin Madina bayan wani samame da aka yi bisa bayanan leƙen asiri daga hukumomin tsaro
- Ado Aliero na ɗaya daga cikin manyan 'yan bindiga da Najeriya ke nema ruwa a jallo saboda hare-hare da garkuwa da Bayin Allah
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Ana rade radin cewa hukumomin Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargi da kasancewa uwa da matar shahararren jagoran ‘yan bindiga a Najeriya, Ado Aliero.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an dade ana neman Ado Aliero ruwa a jallo bisa laifuffuka da dama.

Asali: Getty Images
Rahoton ABC News ya bayyana cewa an kama matan ne a birnin Madina na ƙasar Saudiyya, inda ake zargin suna zaune da sunaye na bogi domin ɓuya ga hukuma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana ganin idan ta tabbata iyalan Aliero ne, kamun na iya zama wata babbar nasara ga Najeriya a yaki da ta’addanci da garkuwa da mutane da ya addabi Arewa maso Yamma.
Yadda aka kama iyalan Ado Aliero a Madina
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron Saudiyya sun gudanar da samamen kama matan ne bisa hadin gwiwa da na Najeriya.
Daily Trust ta wallafa cewa an ce bayanan sirri sun nuna cewa matan suna da alakar ɓoyewa da safarar kuɗi da Ado Aliero.
Samamen da aka yi a birnin Madina na ƙasar mai tsarki, na nuna yadda ake kokarin shawo kan ta’addanci da garkuwa da mutane a matakin ƙetare.
Menene fa'idar kama iyalan Ado Aliero?
Duk da cewa hukumomi ba su bayyana sunayen matan ba a hukumance, majiyoyi sun nuna cewa za su iya bayar da bayanai idan ta tabbata su din uwa da matar Aliero ne.
Ana ganin za su iya bayar da muhimman bayanai game da inda yake da kuma hanyoyin da yake bi wajen samu da kashe kuɗi.
Ana zargin Ado Aliero da jagorantar hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma garkuwa da wasu da dama a jihohin Zamfara, Sokoto da Kebbi.
An dade ana neman Ado Aliero, wanda ya samu karfi wajen yin ta'addanci ta hanyar tara kudin fansa a Najeriya.
Wane matakin bincike za a dauka a gaba?
Ana sa ran cewa hukumomin tsaro na Najeriya za su yi haɗin gwiwa da na Saudiyya domin gudanar da bincike mai zurfi da fitar da gaskiya a game da matan biyu da aka kama.

Asali: Twitter
Ana sa ran idan aka tabbatar da alakar matan da Ado Aliero, za a iya samun wani muhimmin cigaba a kokarin rusa ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ke hana zaman lafiya a yankunan Najeriya.
An kama dan bindiga yana shirin zuwa Hajji
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar DSS ta kama wani da ake zargi dan bindiga ne a filin jirgin sama yana shirin tafiya Saudiyya.
Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin mutumin mai suna Sani Aliyu Galadi da garkuwa da mutane a Najeriya.
Hukumar DSS da sauran jami'an tsaron Najeriya za su cigaba da saka ido a filayen jiragen sama domin tabbatar da masu laifi ba su fita waje ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng