'Babban Laifi ne': Kotu Ta Hana Beli, Ta Tura Fitaccen Mawakin Duniya zuwa Gidan Yari
- An gurfanar da Chris Brown a kotun Manchester bisa zargin kai wa mai shirya waka, Abe Diaw hari da kwalba a gidan rawa a London
- Alkalin kotu ta ce laifin ya fi ƙarfin kotun majistire, don haka ta tura shari’ar zuwa kotun Southwark Crown, tare da ƙin ba da beli mawakin
- Yayin da yake shirin fara zagayen gabatar da wakokinsa a Yuni, ana ganin daure shi na iya hana Chris Brown halartar wasannin da aka tsara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Manchester - An gurfanar da fitaccen mawakin R&B na Amurka, Chris Brown a gaban kotu bisa zargin kai hari da kwalba a wani gidan rawa da ke Landan a shekarar 2023.
An kama mawakin mai shekara 36 a otal ɗin The Lowry da ke Salford a ranar Alhamis, inda daga bisani aka tuhume shi da laifin jikkata mutum ta hanyar amfani da makami.

Asali: Twitter
An gurfanar da fitaccen mawaki a kotu
An zargi Brown, wanda ake kira da Breezy, da kai wa wani mai shirya waka, Abe Diaw, hari da kwalba a gidan rawar Tape da ke garin Mayfair, inji rahoton Sky News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Chris Brown na cikin shirin kaddamar da wakokinsa a Biritaniya, ciki har da wasanni a filin wasa na Co-Op Live da ke Manchester da kuma filin Cardiff’s Principality a watan Yuni da Yuli.
A gaban kotun Majistire da ke Manchester, mai gabatar da ƙara, Hannah Nicholls, ta ce Brown ya aikata laifin "kai farmaki da makamai a cikin gidan rawa ba tare da dalili ba."
Ta shaida wa kotu cewa Chris Brown ya kwadawa Diaw kwalba ba adadi, sannan ya bi shi yana dukan sa da ƙafa da hannu, kamar yadda na’urar CCTV ta ɗauka.
Kotun majistire ta daure mawaki Chris Brown
Rahoton BBC ya nuna cewa Chris Brown ya shigo kotu ne tare da jami’an tsaro. Ya tabbatar da sunansa da ranar haihuwarsa ga kotun amma bai amsa tuhumar ba.
Alkalin kotu, Joanne Hirst, ta ce laifin da ake tuhumar Brown da shi “ya fi ƙarfin” kotun majistire, don haka ta tura shari’ar zuwa kotun Southwark Crown da ke London.
Hirst ta ƙi amincewa da buƙatar beli da lauyoyi Chris Brown suka gabatar, yayin da kotu ta saka ranar 13 ga Yuni a matsayin sabuwar rana don ci gaba da shari’ar.

Asali: Twitter
Wasannin Chris Brown ya shiga ƙila wa ƙala
Wasannin gabatar da wakokin Chris Brown zai fara a ƙasar Holland a ranar 8 ga Yuni, sannan zai yi wasa a Manchester Co-op Live a ranar 15 ga Yuni.
Gabanin zaman kotun, masoyan mawakin sun hallara a wajen kotun domin nuna goyon baya gare shi, sai dai ana ganin daure da aka yi zai hana shi wasa a ƙasar Holland.
A gefe guda, Abe Diaw ya shigar da ƙara kotu, yana neman diyyar dala miliyan 16 (kimanin fam miliyan 12) kan raunuka da Chris Brown ya ji masa.
Kotu ta daure fitaccen mawaki, Portable
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotu ta yanke wa mawaki Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, hukuncin daurin watanni uku a gidan yari.
An kama Portable a watan Maris 2023 bayan da ya buge wani jami’in ‘yan sanda da kuma hana jami’an tsaro aiwatar da aikinsu.
Lauyan gwamnati ya bayyana cewa laifin ya faru ne a ranar 18 ga Nuwamba, 2022 a unguwar Okeosa, Ilogbo, cikin karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng