An Gano Gaskiya, Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Mawakin da Ake Zargin Ya Zagi Annabi SAW
- Kotu ta yanke wa fitaccen mawaki a ƙasar Iran, Amir Hossein Maghsoudloo hukuncin kisa bayan kama shi da laifin taɓa mutuncin Annabi S.A.W
- An gurfanar da mawakin a kotu ne kan tuhume-tuhume da dama, babban shi ne na taɓa mutuncin fiyayyen halitta
- Amir wanda ya yi kaurin suna wajen haifar da ce-ce-ku-ce ya koma zama a Istambul kafin daga bisanni ƴan sandan Turkiyya su miƙa shi ga Iran a 2023
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Wata kotu a ƙasar Iran ta gamsu da hujjojin da aka gabatar gabanta, ta kama Amir Hossein Maghsoudloo da laifin ɓatanci ga Manzon Allah (S.A.W).
Kotun ta yanke wa Amir, mawaƙi wanda aka fi sani da Tataloo hukuncin kisa bayan kama shi wannan laifi na cin mutuncin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W).

Asali: Twitter
Rahoton jaridar Etemad ta ƙasar Iran ta tattaro cewa tun farko an yanke wa fitaccen mawakin hukuncin shekara biyar a gidan yari, amma kotun kolin Iran ta ce ba ta yarda ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun kolin ta goyi bayan mai gabatar da ƙara kan lamarin, wanda ya ce bai amince da hukuncin ɗaurin shekara biyar da aka yankewa Amir kan laifin zagin Annabi ba.
Kotu ta yanke wa mawaki hukuncin kisa
Rahoton ya kara da cewa, "A wannan karon, an yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin kisa saboda ya ci mutuncin Annabi S.A.W."
Tataloo, mai shekaru 37 a duniya, ya kasance yana zaune a Istanbul tun 2018 amma 'yan sandan Turkiyya suƙa mika shi ga hukumomin Iran a watan Disamba 2023.
Tun wannan lokaci yake tsare a kurkukun kasar Iran yana jiran hukuncin da za a yanke masa kan wannan babban laifi da ya aikata a addinin Musulunci.
Tuhume-tuhumen da ake wa mawakin
Baya ga zargin ɓatanci, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari saboda kama shi da laifin tallata karuwanci.
Sauran tuhume-tuhumen da ake yi masa sun hada da yada “farfaganda” a ƙasar Musulunci da kuma buga abubuwan da aka haramta a ƙasar.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: Matasa sun yi tara tara, sun kama malamai 2 da wasu abubuwan ban mamaki
Mawakin dai ya shahara a wajen yin wakokin Rap, pop, da R&B kuma shi mutum ne mai yawan yin abubuwan da suke tayar da ƙura a Iran.
Zanen da aka masa a jikinsa da salonsa ya sa ya shahara a wurin matasan Iran to amma hakan ya sa hukumomi suka sa masa ido tare da bincike kan ayyukansa.
Duk da haka a baya, ƴan siyasa masu ra'ayin rikau a Iran sun rika jawo shi a jiki domin ya taimaka masu wajen jawo hankalin matasa.
Tataloo ya ja hankalin ƴan Iran a 2015 lokacin da ya fitar da wata waƙa don tallafawa shirin nukiliyar Iran, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
A halin yanzu dai, kotu ta yanke mass hukuncin kisa bayan ta kama shi da laifin taɓa mutuncin Annabi Muhammad SAW.
Ɓatanci: An saki Mubarak Bala a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa aan saki Mubarak Bala bayan shafe shekaru hudu a gidan yari sakamakon laifin batanci ga Annabi SAW a Najeriya.

Kara karanta wannan
An gano abin da zai jefa 'yan Najeriya miliyan 13 a talauci a 2025, an gargadi gwamnati
Tun farko dai kotun ɗaukaka ƙara ce ta yi wa Mubarak sassauci a hukuncin da aka yanke masa na zaman gidan gyaran hali tsawon shekaru 24.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng