Biki bidiri: Janet Jackson, Chris Brown da 50 Cent sun cashe a Saudiyya

Biki bidiri: Janet Jackson, Chris Brown da 50 Cent sun cashe a Saudiyya

Rahotanni sun kawo cewa shahararrun mawaka da makadan nan na kasar Amurka sun yi shasu a birnin Jeddah da ke Saudiya, bikin casu da 'yan kasar suka dade suna zuba ido.

An tattaro cewa gudanar da gagarumin bikin casun ne a dandalin Sarki Abdallah da ke birnin Jedda, sannan kuma Daga cikin mawakan da suka cashe sun hada da Janet Jackson, 50 Cent da Chris Brown.

Wannan shi ne bikin casu na farko da aka taba gudanarwa a kasar mai tsarki.

Yan kallo sun yi tururuwan zuwa wajen tare da shewa cikin annashawa cikin sabon yanayi da suka tsinci kansu, saboda shekaru biyu da suka gabata idan aka ce za su samu dama irin haka ba za su taba yarda ba.

Baya ga Fitattun mawakan Amurka an kuma gayyato fitattun mawakan larabawa kamar Tamir Husny da Muhammad Abdou da sauransu.

Hotunan da aka yada a kafafen sadarwa sun nuna Janet Jackson da tawagarta sun yi shiga ba kamar yadda aka saba gani ba ta tsaraici dukkaninsu sanye da bakin tufafi.

Biki bidiri: Janet Jackson, Chris Brown da 50 Cent sun cashe a Saudiyya
Biki bidiri: Janet Jackson, Chris Brown da 50 Cent sun cashe a Saudiyya
Asali: Facebook

Da farko dai Nicki Minaj ce ya kamata ta jagoranci wannan wasa, amma sai ta nuna cewar baza tayi ba saboda rashin nuna goyon bayan 'yan luwadi da madigo da kasar ta Saudiyya take yi.

Nicki Minaj ta yi suna wajen wake-waken batsa da kuma nuna tsiraici a cikin wakokin bidiyonta.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar TUC tayi watsi da tsarin gwamnati kan aiwatar da mafi karancin albashi

Sai dai kuma mawakiyar tayi magana a shafinta na Twitter inda ta bayyana cewa ba tayi haka bane dan ta nuna rashin darajar kasar Saudiyya bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel