Chadi Ta Yanke 'Alaƙa' da Faransa, Tana Shirin Haɗa Kai da Ƙasar Rasha

Chadi Ta Yanke 'Alaƙa' da Faransa, Tana Shirin Haɗa Kai da Ƙasar Rasha

  • Rahotanni na nuni da cewa kasar Chadi ta sanar da yanke alaƙar soji da kasar Faransa bayyan sun dauki shekaru da dama
  • Ministan harkokin wajen Chadi Abderaman Koulamallah ne ya tabbatar da lamarin kuma ya fadi dalilin daukar matakin
  • Biyo bayan ɗaukar matakin, kasar Faransa za ta dauke sojojin da ta jibge a Chadi da suka kai kimanin 1,000 da ma wasu kayan yaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Chad - Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumomin kasar Chadi sun sanar da yanke alaƙar soji da Faransa.

Kasar Chadi ta bayyana cewa Faransa ta kasance ƙawa a gare ta amma lokaci ya yi da za su raba hanya a kan abin da ya shafi soji.

Kasar Chadi
Chadi ta yanke alakar soji da Faransa. Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Legit ta gano matakin da Chadi ta dauka ne a cikin wani sako da kasar ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta sauya magana, ta fadi mamallakin shinkafar 'Tinubu' da aka kama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chadi ta yanke alaƙar soji da ƙasar Faransa

Kasar Chadi ta yanke alaƙar soji da Faransa bayan ministan harkokin wajenta, Abderaman Koulamallah ya gana da takwaransa na Faransa, Jea-Noel Barrot.

Chadi ta shiga sahun kasashen masu magana da Faransanci da suka yanke alakar soji da Faransa bayan Mali, Nijar da Burkina Faso.

Dalilin yanke alaƙar Chadi da Faransa

Abderaman Koulamallah ya bayyana cewa lokaci ya yi da Chadi za ta sake nazari kan hulɗarta da kasashen ketare.

Rahoton Aljazeera ya nuna cewa Abderaman Koulamallah ya ce yanzu haka Chadi ta girma kuma tana son tsayuwa da kafafunta.

Ministan harkokin wajen ya ce bayan shekaru 66 da samun yanci, akwai bukatar Chadi ta samu cikakken iko kan dakarunta.

Yaushe sojojin Faransa za su bar Chadi?

Abderaman Koulamallah ya bayyana cewa za su cigaba da tattaunawa wajen sanya lokacin da sojojin Faransa za su fice daga kasar.

Bincike ya nuna cewa bayan wasu kayan yaki, kasar Faransa tana da sojoji kimanin 1,000 da suke zaune a Chadi.

Kara karanta wannan

Zargin almundahana: Bayan EFCC ta dafe shi, kotu ta yarda a tsare Yahaya Bello

A yanzu haka dai ana hasashen cewa kasar Chadi ta karkata Rasha domin ƙulla alaka bayan kauracewa Faransa..

Tinubu ya yi wa kasar Chadi alkawari

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni sun bayyana cewa mayakan Boko Haram sun fara kwararowa zuwa kauyukan Borno daga yankin Tafkin Chadi.

An ruwaito cewa sojojin kasar Chadi sun tsananta hare-hare kan 'yan ta'addan domin daukar fansar jami'ansu da aka kashe musu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng