Kudin Kwangila: Majalisa Ta Gayyaci Gwamnan CBN, Ministocin Tinubu

Kudin Kwangila: Majalisa Ta Gayyaci Gwamnan CBN, Ministocin Tinubu

  • Rahotanni na nuni da cewa majalisar wakilai ta gayyaci ministocin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki tare da gwamnan CBN
  • Ana bukatar su bayyana dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta kasa biyan wasu ‘yan kwangila hakkokinsu tun shekarar 2024
  • Rahoto ya ce ce matsalar rashin biyan kudin ta jawo asara mai yawa da durkushewar wasu muhimman ayyukan gina kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai ta Najeriya ta ɗauki matakin bincike kan dalilan da suka sa gwamnatin tarayya ta kasa biyan kuɗin da ake bin ta na ayyukan kwangila tun 2024.

Wannan mataki na zuwa ne bayan majalisar ta amince da wani kudiri da aka gabatar da shi a zaman ta na ranar Alhamis.

Majalisa
Majalisa ta gayyaci ministoci kan gaza biyan 'yan kwangila. Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

Leadership ta rahoto cewa daga cikin manyan jami’an da aka gayyata akwai Ministan Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kudi, Abubakar Bagudu; Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Yemi Cardoso; da Akanta Janar na Tarayya, Babatunde Ogunjimi na cikin wadanda aka gayyata.

A cewar majalisar, jami’an gwamnati za su bayyana gaban ta ranar Talata mai zuwa domin bada cikakken bayani kan jinkirin biyan kuɗin da kuma gabatar da jadawalin biyan su nan gaba.

Dalilin gayyatar ministocin Tinubu majalisa

'Dan majalisar wakilai daga jihar Delta, Nnamdi Ezechi, ne ya gabatar da kudirin inda ya nuna damuwa da yadda ‘yan kwangila da dama suka kasa karɓar kuɗinsu.

Hon. Nnamdi Ezechi ya bayyana cewa sun gaza samun kudin ne duk da ayyukan da suka kammala tun watan Oktoba na 2024.

Ya bayyana cewa an ware kuɗi a cikin kasafin shekara ta 2024 domin aiwatar da ayyuka, amma har yanzu ba a biya sama da kashi 50 cikin 100 na kuɗin ba.

Wannan, a cewarsa, ya haddasa dakatar da ayyuka da dama da kuma matsin tattalin arziki ga ‘yan kwangila.

Daily Trust ta rahoto cewa dan majalisar ya ce:

“Rashin biyan ‘yan kwangila ya dakile aiwatar da muhimman ayyukan mazabu.
"Ya rage amincewa da gwamnati, kuma ya rage yawan jarin da ‘yan kasuwa ke shigo da shi a fannin gina kasa.”

Majalisar tarayya na fargabar rikice-rikice

Majalisar ta nuna fargabar cewa idan aka ci gaba da jinkirin, zai iya jawo zanga-zanga, shari’u da kuma durkushewar duk wani aikin raya kasa.

Hon. Ezechi ya jaddada cewa matakin yana shafar al’umma kai tsaye, musamman a yankunan karkara da ke bukatar ayyukan more rayuwa.

Majalisa
Majalisa ta nuna damuwa kan rashin bayan 'yan kwangila. Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Twitter

Saboda haka, majalisar ta umurci kwamitocin hadaka na lissafin kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki da su gudanar da cikakken bincike kan dalilin gaza fitar da kudin.

Rikicin Rivers: Majalisa za ta kafa kwamiti

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta ce za ta kafa kwamiti na musamman domin yin sulhu a jihar Rivers.

Bayan dawowa daga hutun da ta dauka, majalisar ta yanke matsayar yin amfani da dattawan kasa domin shiga lamarin.

Ana fatan hakan zai kawo karshen rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar Rivers wanda ya kai ga dakatar da gwamna Simi Fubara a Maris.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng