Dangote Ya Samu Babban Mukami a Bankin Duniya, Tinubu Ya Taya Shi Murna

Dangote Ya Samu Babban Mukami a Bankin Duniya, Tinubu Ya Taya Shi Murna

  • Shugaba Bola Tinubu ya taya Aliko Dangote murna bisa nadin da Bankin Duniya ya yi masa a kwamitin zuba jari a harkokin kasuwanci
  • Tinubu ya ce nadin ya dace da cancantar Dangote, la’akari da irin gudunmuwar da attajirin ya bayar ta fuskar zuba jari da samar da ayyukan yi
  • Dangote zai yi aiki tare da manyan shugabannin kamfanoni na duniya domin samar da hanyoyin jawo zuba jari a kasashen da ke tasowa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya taya Aliko Dangote murna bisa nadin da Bankin Duniya ya masa a babban kwamitin da ke da alhakin habaka zuba jari da samar da ayyuka.

Tinubu ya bayyana nadin a matsayin wani mataki da ya dace da matsayin Dangote, la’akari da gagarumar gudunmuwar da ya bayar wajen ci gaban harkokin kasuwanci a Afirka.

Dangote
Tinubu ya taya dangote murnar samun mukami a bankin duniya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Legit ta tattaro bayanan da Bola Tinubu ya yi ne a cikin wani sako da fadar shugaban kasa ta wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana Dangote a matsayin jarumin da ya samar da sababbin hanyoyin bunkasa tattali ta hanyar kasuwancinsa.

Bola Tinubu ya nuna kwarin gwiwa kan Dangote

Shugaba Tinubu ya bukaci Dangote da ya yi amfani da wannan dama wajen amfani da dabarunsa da tunaninsa na kawo canji domin amfanar da kasuwannin da ke tasowa a duniya.

Dangote ya shiga cikin sabon tsarin fadada kwamitin zuba jarin Bankin Duniya, wanda zai mai da hankali kan jawo zuba jari da samar da ayyuka a kasashe masu tasowa.

Kwamitin na kunshe da fitattun shugabannin kasuwanci da suka hada da Shugaban Kamfanin Bayer AG, Bill Anderson.

Haka zalika shugaban Bharti Enterprises, Sunil Bharti Mittal; da Shugaban Kamfanin Otal-otal na Hyatt, Mark Hoplamazian na cikin kwamitin.

Tinubu ya ce Dangote ya kafa tarihi a Afrika

Tinubu ya yaba da yadda Dangote ya kasance kan gaba a nahiyar Afirka wajen habaka tattali da ci gaba da zuba jari a fannoni da dama.

Dangote na da harkokin kasuwanci da suka hada da samar da siminti, taki, gishiri, sukari, da man fetur.

Matatar Dangote mai darajar Dala biliyan 20, ita ce mafi girma a Afirka kuma ita ce gagarumar kadarar kamfanin Dangote.

Matatar Dangote
Matatar da Dangote a kafa a Legas. Hoto: Dangote Industries.
Asali: UGC

Bankin Duniya ya ce sabon tsarin da aka shigar da Dangote ciki na nufin hada kai da shugabannin da suka shahara wajen samar da ayyukan yi.

Dangote da abokan aikin shi a Bankin Duniya za su yi aiki domin taimakawa bunkasa tattalin arzikin kasashe masu tasowa.

Tinubu ya jaddada cewa Najeriya na alfahari da irin matsayin Dangote na kasa da kasa, yana mai fatan wannan dama za ta kara bunkasa cigaban duniya baki daya.

Shugaba Tinubu ya yi ta'aziyyar Sheikh Hadiyyatullah

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar babban malamin Musulunci Abdur Rasheed Hadiyyatullah Iwo.

Bola Tinubu ya ce Sheikh Abdur Rasheed Hadiyyatullah Iwo malami ne da ya yi tsayuwar daka wajen yada addini.

Baya ga haka, Bola Tinubu ya bayyana cewa Sheikh Hadiyyatullah Iwo ya ba shi gudumawa a lokacin da yake neman mulki a 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng