'Ka Dawo da Komai da Ke Wurinka': Gwamna Ya Dakatar da Sarki a Adamawa

'Ka Dawo da Komai da Ke Wurinka': Gwamna Ya Dakatar da Sarki a Adamawa

  • Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya dakatar da Sarkin Daware, Alhaji Hassan Ja’afaru, ba tare da kayyade lokaci ba bisa zargin cin hanci da gazawar shugabanci
  • A cewar wasikar da Adama Mamman ya rattaba hannu, an umarci sarkin da ya mika duk kadarorin gwamnati dake hannunsa ga sakataren yankin
  • Wasikar ta bayyana cewa an samu Ja’afaru da laifin kwace gonaki, kin zama cikin masarautarsa da kuma barazana ga zaman lafiya
  • Fintiri ya ce ba za a kyale wani bangare ba wajen yaki da cin hanci da rashawa a fadin jihar Adamawa, koda na gargajiya ne

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa- Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya dakatar da basarake saboda wasu zarge-zarge.

Gwamna Fintiri ya ɗauki matakin kan Sarkin Daware, Alhaji Hassan Ja’afaru, ba tare da kayyade lokaci ba.

Gwamna ya dakatar da Sarki a Adamawa
Gwamna Fintiri ya dakatar da Sarkin Daware a Adamawa. Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri.
Asali: Twitter

A wasikar da aka sanya ranar 25 ga Afrilu, 2025, da Adama Mamman ya rattaba hannu, an umarce shi ya mika duk kadarorin gwamnati, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban karamar hukumar Fufore ya rasu

Rahoton Legit Hausa ya ruwaito cewa shugaban karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, Hon. Shuaibu Babas, ya rasu bayan fama da doguwar rashin lafiya da ya dade yana yi.

Marigayin ya taba wakiltar mazabar Fufore/Gurin a majalisar dokokin jihar da kuma zama shugaban riko na hukumar ci gaba na Malabu.

Bayan rasuwarsa, an yi masa jana'iza bisa koyarwar addinin Musulunci kamar yadda aka saba.

Marigayin ya bar matansa, 'ya'yansa da kuma 'yan uwansa waɗanda suka yi juyayin rasuwarsa da addu'ar Allah ya jikansa da rahama.

Gwamna ya dakatar da Sarki a Adamawa
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya dakatar da Sarkin Daware a Adamawa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Wanene Ja'afaru da aka dakatar?

Ja’afaru wanda shi ne tsohon hakimin Daware a karamar hukumar Fufore, an bincike shi kuma an same shi da laifin cin hanci da gazawa a shugabanci.

Sashen wasikar ya ce:

"Sakamakon koke-koke da aka shigar kan cin hanci, gazawa, da barazana ga tsaro, an dakatar da kai daga aiki.
"Kana da alhakin mika duk kadarorin gwamnati dake hannunka ga sakataren yankin har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.
"Yakin da nake yi da cin hanci a jihar Adamawa ba zai bar kowanne bangare ba, ciki har da na gargajiya."

Legit Hausa ta tattauna da matashi

Mubarak Muhammad da ke zaune a garin ya ce matakin ya yi idan har an tabbatar da abin da ake zargin basaraken.

"Daman bai kamata wani yafi ƙarfin doka komai girmansa fatan dai a kammala bincike domin gano gaskiya kan zargin da ake yi masa."

- Cewar Mubarak

Ikon gwamnoni wajen nadi da tsige sarakuna

A Najeriya, gwamnoni na da ikon nada ko tsige sarakunan gargajiya bisa tsarin mulki da dokokin da aka tanada a kowace jiha.

Wannan iko yana fitowa ne daga matsayin gwamnoni a matsayin shugabannin jihohi da masu kula da zaman lafiya da daidaito a cikin al’umma.

Kowane yanki yana da dokar sarauta wacce ke tsara yadda ake nadin sarki da yadda ake tsigeshi idan ya saba wa ka’ida.

A mafi yawan lokuta, idan aka samu koke-koke ko zarge-zarge na gazawa a shugabanci, cin hanci, ko tayar da fitina daga wani sarki, gwamnati kan kafa kwamitin bincike domin tabbatar da gaskiya.

Bayan bincike, idan an tabbatar da laifuka, gwamna zai fitar da umarni na tsige sarkin ba tare da wata matsala ba, domin kare zaman lafiya da doka a jihar.

Duk da cewa ana baiwa majalisun sarakuna shawara a wasu lokuta, hukuncin karshe na nadin sabon sarki ko tsige tsoho yana hannun gwamna.

Irin wannan iko ya sha amfani a Najeriya, inda gwamnoni daban-daban suka tsige sarakuna saboda dalilai masu kama da rashin bin doka ko gazawa wajen jagoranci jama'a yadda ya kamata. Wannan tsarin na daga cikin matakan kare martaba da ci gaban al’umma.

Gwamna Fintiri ya horas da matasa a Adamawa

Kun ji cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya ƙaddamar da shirin koyon sana’o’i domin bai wa matasa da mata horo a fannoni daban-daban na rayuwa.

Gwamnatin jihar ta farfaɗo da cibiyoyin koyon sana’o’i guda 10 tare da samar da kayan aikin zamani domin ba da horo mai inganci.

An zaɓi sana’o’in ne bisa bukatun kasuwar aiki, don bai wa mahalarta damar samun aiki ko kafa nasu kasuwancin a Adamawa da fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.