Amurka Ta Saka Ranar Fitar da Bayanan 'Sirri' game da Bola Tinubu

Amurka Ta Saka Ranar Fitar da Bayanan 'Sirri' game da Bola Tinubu

  • Wata kotu a Amurka ta umurci FBI, CIA da sauran hukumomi da su saki rahotannin binciken da suka yi kan Bola Tinubu
  • A ranar 2 ga Mayun 2025 duniya za ta iya samun wadannan bayanai a araha bayan tsawon shekaru ana jifansa da zargi
  • Rahoton ya shafi zargin da aka yi wa shugaba Bola Tinubu da wasu mutane da alaka da harkar miyagun kwayoyi a shekarun baya
  • Tun a lokacin da aka dawo da maganar, fadar shugaban kasa ta ce babu abin boyewa a bayanan kuma ba su nuna laifin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka - Wasu manyan hukumomin leken asiri da bincike na gwamnatin Amurka sun shirya fitar da rahotannin binciken da suka shafi Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa bayanan sun shafi zargin alaka da safarar miyagun kwayoyi a shekarun baya da aka yi wa Tinubu.

Bola Tinubu
Amurka ta saka ranar fitar da bayanan da suka shafi Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Donald J Trump
Asali: Facebook

Rahoton ya fito ne daga jaridar Premium Times, inda ta ce alkalin kotun, Beryl Howell, ya bayyana cewa kin sakin bayanan “ba abin yarda ba ne.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin kotu a birnin Washington DC ya bayar da umarnin sakin bayanan, inda ya umurci a saki duk wasu bayanan da suka danganci binciken a ranar Juma’a, 2 ga watan Mayu, 2025.

Hukumomin Amurka da bayanan suka shafa

Hukumomin da aka umurta da sakin rahotannin sun hada da:

  • Ofishin Lauyoyin Gwamnatin Tarayya
  • Hukumar FBI
  • Hukumar Kula da Haraji (IRS)
  • Hukumar Hana Safarar Miyagun Kwayoyi (DEA)
  • Ma’aikatar Harkokin Waje
  • Hukumar Leken Asiri ta CIA

Sai dai duk da haka, an ruwaito cewa alkalin kotun ya ware hukumar CIA daga wajibcin sakin bayanan.

Wannan shari’a dai an shigar da ita ne tun watan Yunin 2023 ta hannun wani ɗan Amurka mai suna Aaron Greenspan karkashin dokar samun bayanai ta FOIA.

bola Tinubu da wadanda lamarin ya shafa

Aaron Greenspan ya bukaci rahotanni daga binciken da aka gudanar tsakanin FBI, IRS, DEA da sauran ofisoshin lauyoyi na Amurka.

Ya nemi bayanai kan wasu mutum hudu da ake zargin suna da alaka da wata kungiyar safarar miyagun kwayoyi:

  • Shugaba Bola Tinubu
  • Lee Andrew Edwards
  • Mueez Akande da
  • Abiodun Agbele
Tinubu
Tinubu ya shiga cikin mutane 4 da za a fitar da bayanansu a Amurka. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Duk da haka, jaridar Daily Trust ta wallafa cewa lauyoyin da ke shari’ar sun ce ana da damar daukaka kara dangane da wannan umarni na kotu.

Fadar shugaban kasa ta musanta zargin

A martanin da ta fitar, fadar shugaban kasa ta ce bayanan da ake kokarin fitarwa ba sababbi ba ne kuma ba su kunshi wani hukunci da ke nuna cewa Tinubu ya aikata laifi ba.

Ta ce babu wani sabon abu a ciki da zai iya bata sunan shugaban kasa ko kuma kawo masa tawaya a fagen siyasa.

Tuhume-tuhume kan Tinubu

​Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na fuskantar jerin muhimman rikice-rikice da suka shafi siyasa, tattalin arziki, da kuma amincin jama'a tun bayan hawansa mulki a 2023.

Baya ga batun takardun karatu da ake ci gaba da bincike a kansu, akwai wasu muhimman matsaloli da suka janyo cece-kuce a cikin gida da waje.​

A fannin tattalin arziki, cire tallafin man fetur da kuma sauya tsarin musayar kudin waje sun haifar da hauhawar farashin kayayyaki da tashin gwauron zabi na kudin naira.

Hakan ya jefa miliyoyin 'yan Najeriya cikin matsin rayuwa, inda hauhawar farashin kayayyaki ya kai sama da kashi 30% a cikin shekara guda. ​

A bangaren tsaro, hare-haren 'yan ta'adda da rikice-rikicen kabilanci sun sake karuwa a yankunan Arewa, musamman a jihohin Benue da Filato, inda aka samu mutuwar mutane sama da 150 a watan Afrilu 2025. ​

Baya ga haka, gina titin gabar teku daga Legas zuwa Calabar ya jawo cece-kuce kan yadda aka raba kwangilar aikin da kuma yawan kudin da za a kashe, wanda ya kai kusan Naira tiriliyan 15. ​

Amurka ta kama wasu 'yan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta cafke wasu 'yan Najeriya sama da 20 kan zargin damfara.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin matasan da shigar karya a kafafen sada zumunta suna nuna su mata ne suna damfarar turawa.

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa laifin ya jawo mutuwar matasa da dama da aka damfara tare da asarar dukiya mai yawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng