Tinubu Ya Yi Ta'aziyyar Babban Malamin da Ya ba Shi Gudumawa a Zaben 2023

Tinubu Ya Yi Ta'aziyyar Babban Malamin da Ya ba Shi Gudumawa a Zaben 2023

  • Bola Tinubu ya bayyana alhini kan rasuwar Sheikh Abdur Rasheed Hadiyyatullah Iwo, shugaban babbar majalisar shari’ar Musulunci a Najeriya
  • Shugaba Tinubu ya ce Sheikh Hadiyyatullah ya rayu cikin hidimar addini da jin ƙai, inda ya jagoranci majalisar shari'a a gaskiya da rikon amana
  • Marigayin zai ci gaba da kasancewa abin koyi ga al’umma, musamman wajen yaɗa zaman lafiya, adalci da daidaito a tsakanin mabiya addinai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jimaminsa bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abdur Rasheed Hadiyyatullah Iwo.

Kafin rasuwar shi, Sheikh Abdur Rasheed Hadiyyatullah Iwo shi ne shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya.

Tinubu
Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Sheikh Hadiyyatullah. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanin da Bola Tinubu ya yi ne a cikin wani sako da fadar shugaban kasa ta wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Hadiyyatullah ne ya jagoranci makarantar koyar da shari’ar Musulunci ta Sheikh Ibn Baz Shariah College da ke garin Iwo, Jihar Osun bayan kafa ta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Sheikh Abdur Rasheed Hadiyyatullah ya rasu yana da shekaru 81 a duniya.

Tinubu ya yaba da irin gudumawar malamin

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, Tinubu ya bayyana Sheikh Hadiyyatullah a matsayin malami nagari.

Tinubu ya ce malamin ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar Musulunci da al’umma:

“A matsayinsa na shugaban Majalisar Shari’ah, ya yi shugabanci mai nagarta da ke cike da hangen nesa.
"Ya rayu bisa koyarwar Allah da ManzonSa (SAW), kuma ya shahara da taimakon al’umma ta hanyar makarantar shari’ar da ya kafa.”

Tinubu ya kuma tuna irin goyon bayan da majalisar ta ba shi a lokacin zaɓen 2023, inda suka tsaya a kan gaskiya da adalci tare da kin amincewa da yaɗa ƙarya da ƙage.

'An yi babban rashi a cikin al’umma' – Tinubu

Tinubu ya bayyana rasuwar Sheikh Hadiyyatullah a matsayin babban gibi ga Musulman Najeriya, yana mai cewa za a yi kewar ilimi da jajircewarsa wajen yaɗa addini da zaman lafiya.

Ya taya iyalansa, mutanen Iwo da dukkan mabiya addinin Musulunci a Najeriya alhini bisa rashinsa, yana mai bayyana marigayin a matsayin abin koyi ga kowa da kowa.

Shugaban ƙasa ya kuma bukaci Majalisar Shari’ar Musulunci da ta ci gaba da riƙe tutar gaskiya da adalci da marigayin ya rayu da su.

Shugaba Tinubu ya roƙawa malamin gafara

A ƙarshe, Tinubu ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa Sheikh Hadiyyatullah, Ya jikansa, Ya kuma saka masa da Aljannar Firdausi.

Punch ta wallafa cewa ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba iyalan marigayin da sauran al’umma juriyar wannan rashi da juriya da ƙarfin gwiwa a wannan lokaci na jimami.

Mahaifiyar Sheikh Asadussunnah ta rasu

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya rasa mahaifiyar shi a jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa mahaifiyar malamin ta rasu ne a ranar Litinin, 28 ga watan Afrilun shekarar 2025.

Tun bayan mata jana'iza kamar yadda Musulunci ya tanadar, malamai da sauran 'yan uwa sun fara yi wa Sheikh Asadussunnah ta'aziyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng