Dangote Ya Fadi Gidajen Mai 6 da ake Samun Fetur a Sabon Farashinsa Mai Sauki
- A ranar Laraba matatar Dangote ta sanar da rage farashin man fetur ga ‘yan kasuwa da kuma abokan hulɗarta a fadin Najeriya
- Ga ‘yan kasuwa, Dangote ya rage farashi da N30, yayin da abokan hulɗar shi ma suka saukar da farashin da ake sayar wa jama’a
- Sauke farashin da ake samu ya zama abin farin ciki ga ‘yan Najeriya, inda ake sa ran karin saukin farashin man fetur gaba kadan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Matatar Dangote ta bayyana gidajen man da 'yan Najeriya za su rika sayen mai a kan farashinta.
Hakan na zuwa ne bayan matatar ta yanke shawarar rage farashin litar mai daga N865 zuwa N835 ga abokan huldarta.

Asali: Getty Images
Legit ta gano bayanin ne a cikin wata sanarwa da aka wallafa a X da shugaban sashen talla da hulda da jama’a na Dangote Group, Anthony Chiejina ya rattabawa hannu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Anthony Chiejina ya bayyana cewa an yi ragin ne domin rage wa ‘yan Najeriya nauyin wahalar rayuwa.
Ga cikakken jerin sunayen ‘yan kasuwar man fetur da ke sayar da fetur ɗin Dangote a sabon farashin N835:
- MRS Oil
- AP (Ardova)
- Heyden Petroleum
- Optima Energy
- Hyde Energy
- Tecno Oil
Farashin Dangote a yankunan Najeriya
A cikin sanarwar, Dangote ya bayyana cewa a yankin Kudu maso Yamma, farashin lita zai kasance N900, daga N930.
A yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya kuma, farashin lita zai kasance N910, daga N940.
A Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da Arewa maso Gabas, farashin zai sauka zuwa N920 daga N950.
Chiejina ya bayyana cewa matatar na aiki kafada da kafada da ‘yan kasuwa domin tabbatar da cewa an saukar da farashin da adalci a faɗin ƙasar.
Sashe na sanarwar ya ce:
“Wannan saukin farashin ya sake tabbatar da jajircewarmu wajen samar da man fetur mai inganci a farashi mai sauƙi, wanda zai amfani 'yan ƙasa.
"Bugu da ƙari, muna aiki tare da abokan hulɗarmu domin tabbatar da cewa raguwar farashin ta isa ga kowane yanki yadda ya kamata.”

Asali: Getty Images
Saukar farashin dizil a Najeriya
Baya ga rage farashin fetur, Dangote ya bayyana cewa an samu gagarumar raguwa a farashin dizil da iskar gas (LPG) saboda ci gaba da ƙoƙarin da matatar ke yi.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“Matatar Dangote ta jajirce wajen saukar da farashin fetur da sauran kayan da take tacewa, domin ci gaba da amfanar 'yan Najeriya.
“Muna da yakinin cewa rage farashin zai yi tasiri a tattalin arziki, tare da kawo sauki wa ‘yan ƙasa da kuma tallafa wa ci gaban tattali, musamman a lokacin bukukuwan Easter.”
Matatar ta kuma tabbatar da aniyar ta na ci gaba da samar da kayayyakin mai masu inganci, tare da samar wadataccen mai a ko da yaushe.
Legit ta tattauna da dan acaba
Wani mai aikin acaba a jihar Gombe, Muhammad Ibrahim ya zantawa Legit cewa suna kira ga NNPCL ya sauke farashi kamar yadda Dangote ya yi.
Muhammad Ibrahim ya ce:
"Ko da Dangote ya sauke farashi ba a kowane lokaci yake shafar mutane a kan lokaci ba. Amma da NNPCL zai sauke farashi, da kowa zai shaida a Najeriya cikin kankanin lokaci."
Masu matatu sun ce man fetur zai sauka
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar masu matatun mai ta kasa ta ce akwai alamun cewa za a cigaba da sumun saukin man fetur a Najeriya.
Kungiyar ta ce akwai yiwuwar samun saukin litar man fetur har zuwa kasa da N400 a bisa hasashensu.
Masu matatun mai sun ce saukar farashin danyen mai a kasuwar duniya ne zai janyo karyewar litar man fetur a fadin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng