A karshe: Donald Trump ya saduda, ya karbi faduwa tare da yin gargadi

A karshe: Donald Trump ya saduda, ya karbi faduwa tare da yin gargadi

- Bayan an kai ruwa rana, shugaba Trump na kasar Amurka ya yarda cewa Sanata Joe Biden ya kayar da shi

- Trump ya ki yarda cewa Sanata Biden ya kayar da shi duk da sakamakon zabe ya nuna hakan

- Tun kafin a gudanar da zabe Trump ya ki amsa tambayar ko zai mika mulki idan ya fadi zaben kujerar shugaban kasa a Amurka

A karshe, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya amince cewa ya sha kaye a hannun abokin hamayyarsa, Sanata Joe Biden.

A wani sako da ya wallafa ranar Lahadi, Trump ya yarda Biden ya samu nasara amma ta hanyar tafka magudin zabe.

"Ya samu nasara ne saboda an tafka magudi a zaben. Babu masu sa-ido, babu masu lura da zabe. An yi amfani da wani kamfani da sunansa ya gurbata wajen tattara sakamakon zabe. Kafafen yada labarai da ke yada labaran bogi, da wadanda suka yi shiru, suka ki yin magana, duk sun taimaka wajen danne nasarar da na samu a Texas," kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Trump ya yi ikirarin samun nasara a daren da aka kammala zaben shugaban kasar Amurka.

KARANTA: Matashi ya kashe dukkan mutanen gidansu bayan ya gano shi dan riko ne

A cikin mako ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa sakataren gwamnatin ƙasar Amurka, Mike Pompeo, a ranar laraba, ya ce ƙasar Amurka zata yi amfani da dukkan makaman da take dasu don yaƙar ta'addanci a Najeriya da yammacin Afirika.

A karshe: Donald Trump ya saduda, ya karbi faduwa tare da yin gargadi
Biden da Trump
Asali: UGC

Pompeo ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da haɗakar kasashen duniya (GCD) don cin galabar ƙungiyar ISIS wanda ƙasar Najeriya ta kasance mai masaukin baƙi.

KARANTA: Bayan shekara dubu uku, an gano wata siffa a sansanin da sojojin Annabin Dauda suka mamaye a Golan

Acewarsa, An samu gagarumar nasara a tattaunawar ganawa da gwamnatin Najeriya.

Sakataren na gwamnatin Amurka ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa; "an samu gagarumar matsaya da nasara a tattaunawa da gwamnatin Najeriya a taron haɗakar ƙasashen duniya don cin galabar ISIS da makamantan ƙungiyoyi irinta a ko ina a faɗin duniya. Ina godiya ga Najeriya da ta ɗauki nauyinn taron."

A taron, Ƙasar Amurka da takwarorinta, ƙasashe 82, mambobin haɗakar kasashen sun nuna zummar son ganin an kawo ƙarshen ISIS, Boko Haram da sauran manyan ƙungiyoyin ƴan ta'adda na duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel