Fafaroma Francis Ya Rasu a Vatican, an Bayyana Cutar da Ta Zama Ajalin Shi
- An sanar da rasuwar Fafaroma Francis a safiyar Litinin ana tsaka da bikin Easter bayan fama da cutar numfashi da ta shafi huhun shi
- Fafaroman ya rasu ne da misalin ƙarfe 7:35 na safe a Casa Santa Marta, inda ya kwashe kwanaki bayan dawowa daga asibiti yana jinya
- An ruwaito cewa Fafaroma Francis ya shafe rayuwarsa yana ayyukan addinin Kirista da kuma hidima ga mabukata da marasa galihu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Italy - Mai kula da harkokin Vatican bayan mutuwar Fafaroma, Cardinal Kevin Farrell, ya sanar da rasuwar Fafaroma Francis da misalin ƙarfe 9:45 na safiyar Litinin.
Daukacin mabiya cocin Katolika da mabiya addinin Kirista sun shiga jimami bayan mutuwar babban jagoran addinin.

Asali: Getty Images
Legit ta tattaro bayanai kan rasuwar da shirye shiryen birne Fafaroma Francis ne a cikin sanarwar da kafar Vatican News ta fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar:
“Fafaroma Francis, ya koma ga mahalicci a safiyar yau da misalin ƙarfe 7:35. Rayuwarsa gaba ɗaya ta kasance cike da hidima ga Ubangiji da cocinsa.”
Cutar da ta yi ajalin Fafaroma Francis
An kwantar da Fafaroma Francis a Asibitin Agostino Gemelli ranar 14 ga Fabrairu, 2025, bayan fama da matsanancin mura da wata cutar numfashi.
Daga bisani, likitoci sun gano cewa yana ɗauke da ciwon huhu mai tsanani (bilateral pneumonia) ranar 18 ga Fabrairu.
Bayan kwana 38 yana jinya, Fafaroman ya koma Vatican, inda ya ci gaba da jinya a Casa Santa Marta har zuwa karshen rasuwarsa a yau Litinin.
Bayani kan rayuwar Fafaroma Francis
Fafaroma Francis da aka haifa a ƙasar Argentina da sunan Jorge Mario Bergoglio, ya yi fama da rashin lafiya tun yana matashi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi masa tiyata yana matashi don cire wani ɓangare na huhunsa da cutar numfashi ta shafa.
Tun daga wancan lokaci, ya kasance yana fama da rashin lafiya da ke da alaka da numfashi. Har ma a shekarar 2023 ya soke wata ziyara zuwa UAE saboda cutar mura da kumburin huhu.
A watan Afrilu 2024, Fafaroman ya amince da sabon kundin jagorar gudanar da jana’izarsa wanda zai kasance cikin tsari mai sauƙi.
An zabi yi masa jana'iza mai sauki ne domin nuna cewa ya karkare rayuwarsa a matsayin mai bishara, ba a matsayin mai iko ba.

Asali: Facebook
Karin bayani kan jana'izar Fafaroma Francis
A cewar shugaban al’amuran ibada na Vatican, Diego Ravelli Fafaroman ya buƙaci masa jana’iza mai sauƙi da natsuwa domin nuna ban gaskiyar Kiristanci kan rayuwa bayan mutuwa.
Sky News ta rahoto cewa Diego Ravelli ya ce:
“Sabon tsarin jana’izar zai ƙarfafa fahimtar cewa Fafaroma ba wani mai iko ba ne, sai dai mai bishara kawai kuma mabiyin Kiristi,”
An ba da hutun bikin Easter a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta ba da hutun kwanaki domin bukukuwan Good Friday da Easter Monday.
Sanarwar gwamnatin ta bayyana cewa an ba da hutun ne domin Kiristoci su samu damar yin bukukuwa cikin nitsuwa a Najeriya.
Baya ga haka, an bukaci Kiristocin Najeriya da su yi addu'o'i domin ganin an samu hanyoyin magance matsalolin da suka addabi kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng