Ana Fama da Rashin Tsaro, Zanga Zanga Ta Barke a Katsina, an Ji Dalili

Ana Fama da Rashin Tsaro, Zanga Zanga Ta Barke a Katsina, an Ji Dalili

  • Wasu matasa a jihar Katsina sun fito kan tituna domin nuna adawarsa kan ayyuan rundunar tsaro ta jihar (C-Watch)
  • Matasan sun gudanar da zanga-zangar ne a ranar Asabar da safe bayan mambobin sun ji wa wani matashi rauni bayan sun samu saɓani
  • Jami'an tsaro sun shiga cikin lamarin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya faru

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - An samu ɓarkewar wata zanga-zanga a garin Radda da ke ƙaramar Charanchi ta jihar Katsina.

Zanga-zangar ta auku ne bayan wani rikici da ya ɓarke tsakanin wani mazaunin yankin, Mustapha Ahmed, da wasu mambobin rundunar tsaro ta jihar Katsina (C-Watch).

An yi zanga-zanga a Katsina
Matasa sun yi zanga-zanga a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa sun yi zanga-zanga a Katsina

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, lokacin da Mustapha Ahmed, mai shekara 40, ya samu saɓani da mambobin C-Watch, wanda hakan ya jawo suka yi masa rauni a jikinsa.

Bayan faruwar lamarin, an garzaya da Ahmed zuwa asibitin gwamnati na Dutsinma domin kula da lafiyarsa.

Amma saboda tsananin raunin da ya samu, daga bisani aka mayar da shi asibitin koyarwa na tarayya da ke Katsina domin ci gaba da jinya.

Sai dai, a ranar Asabar, 19 ga watan Afrilu, wasu matasa daga garin Radda sun fito zanga-zanga da safe, suna buƙatar a ɗauki mataki kan yadda mambobin C-Watch ke gudanar da ayyukansu a yankin.

Matasan sun bayyana damuwarsu bisa yadda ake cin zarafin jama’a da sunan ayyukan samar da tsaro.

Jami'an tsaro sun shiga lamarin

Jami'an 'yan sanda
Wasu matasa sun fito zanga-zanga a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jami’an tsaro sun isa wurin zanga-zangar da gaggawa domin shawo kan lamarin.

A jawabinsa ga masu zanga-zangar, DPO na ƴan sanda ya buƙace su da su ci gaba da bin doka da oda, tare da tabbatar musu cewa an karɓi ƙorafinsu kuma za a bi diddigin batun yadda ya kamata.

Hakimin garin Radda, Alhaji Kabir Umar Barebari, shi ma ya shiga tsakani kan lamarin, inda ya yi alƙawarin mika ƙorafin zuwa ga hukumomin da abin ya shafa domin samun mafita.

Bayan shawo kan lamarin cikin lumana, masu zanga-zangar sun watse cikin kwanciyar hankali ba tare da wani tashin hankali ba.

Hukumomi na ci gaba da sa ido a kan lamarin yayin da bincike ke gudana domin gano ainihin musabbabin rikicin da ya auku tsakanin Mustapha Ahmed da mambobin C-Watch.

Akwai sharri a ciki

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani jami'in C-watch a garin Radda wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Ya bayyana cewa an bugi matashin ne bayan ya daɗe yana yin kalamai marasa daɗi kan jami'ansu.

"Eh don duka an buge shi amma batun sumar da shi wannan sharri ne kawai da kuma yunƙurin ɓata mana suna."

- Jami'in C-watch

Ƴan sanda sun ƙi karɓar cin hanci a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun samu nasarar cafke wasu ɓarayin mota mutum biyu.

Mutanen biyu da ake zargin cewa ɓarayin mota ne sun yi yunƙurin ba ƴan sanda cin hancin N1m domin su toshe musu baki.

Binciken farƙo da aka gudanar ya nuna cewa motar da mutanen biyu ke ciki an sato ta ne daga babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng