Shugaban China Ya Bukaci Lalata Nukiliyar Amurka da Sauran Kasashe
- Shugaban China, Xi Jinping, ya bukaci a haramta makaman nukiliya gaba daya tare da lalata dukkan wadanda ake da su
- Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce hadin gwiwar kasashen Rasha, Amurka da China na iya karfafa zaman lafiyar duniya
- Shi kuwa shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana taron shugabannin kasashen uku a matsayin wani abu da zai shiga tarihi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Shenzhen, China – Shugabannin kasashen China, Rasha da Amurka sun bayyana matsayoyinsu kan makaman nukiliya, tsaron duniya da hadin gwiwar kasashen uku a wani taron koli na musamman da suka gudanar a birnin Shenzhen na China.
Shugaban China, Xi Jinping, ya yi kira da a haramta makaman nukiliya baki daya tare da lalata su, yayin da shugabannin Rasha da Amurka, Vladimir Putin da Donald Trump, suka jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin kasashen.

Source: Getty Images
Xi ya bukaci a lalata nukiliya
Al Jazeera ta rahoto Xi Jinping ya ce ya kamata a haramta makaman nukiliya gaba daya tare da lalata su domin gina duniya da ba ta da irin wadannan makamai.
Kamfanin dillancin labaran China na Xinhua ya ruwaito shi yana cewa yakin nukiliya ba zai yi nasara ba, kuma bai kamata a taba yinsa ba.
Ya kara da cewa dole ne a dauki dukkan matakan da suka dace domin hana barkewar irin wannan yaki.
Xi ya kuma bukaci kasashen uku su kara hadin gwiwa wajen tabbatar da tsaron makamashi da daidaiton hanyoyin samar da makamashi a duniya.
Maganar da Putin ya yi
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana cewa Rasha, Amurka da China za su iya taimakawa wajen karfafa zaman lafiyar duniya idan suka hada kai cikin kyakkyawar fahimta.
Putin ya ce ya kamata shi da Xi da Trump su tattauna batutuwan da suka shafi duniya da yankunansu, da kuma tsaron makamashi.
Ya kuma bayyana cewa ganawarsa ta baya da Trump ta fi mayar da hankali kan yakin Ukraine, bisa bukatar shugaban Amurka.
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Rasha na TASS ya ruwaito Putin yana cewa kasashen uku ba wai kawai sun yi nasara a yakin duniya na biyu ba ne, har ma suna da nauyin tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Source: Getty Images
Trump ya ce sun shiga tarihi
A nasa jawabin, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana taron a matsayin wata ganawa ta tarihi tsakanin manyan kasashe uku a duniya.
Rahoton BBC ya nuna cewa Trump ya ce kasashen Amurka, Rasha da China suna da manyan makaman nukiliya guda uku mafi girma a duniya.
Ya kara da cewa: “Mun kafa tarihi,” yana magana kan muhimmancin taron da shugabannin kasashen uku suka gudanar.
Putin ya je China da jakar nukiliya
A wani labarin, mun rahoto cewa an ga wani jami’in sojan ruwan Rasha dauke da jakar makaman nukiliya ta kasar gabanin taron shugabannin Rasha, Amurka da China.
Jakar mai suna Cheget na bai wa manyan jami’an Rasha damar ba da umarnin harba makaman nukiliya daga nesa, kuma ana tabbatar da cewa tana kusa da shugaban kasar.
Ana sa ran shugabannin kasashen uku za su tattauna batutuwan da suka shafi yakin Iran da Ukraine, makaman nukiliya da kuma tsaron duniya a taron da aka gudanar a ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng

